’Yan ta’adda na kokarin kafa sansani a Taraba —Gwamna Darius

Gwamnan ya ja hankalin jami’an tsaro da su kasance cikin shiri.

’Yan ta’adda na kokarin kafa sansani a Taraba —Gwamna Darius

Gwamnan Jihar Taraba, Darius Ishaku

Gwamnan Jihar Taraba Darius Ishaku, ya yi kira ga jami’an tsaro cewar ’yan ta’adda na kokarin kafa sansaninsu a jiharsa.

Gwamnan ya yi sanarwar ne jim kadan bayan sanya wa kasafin 2022 hannu a garin Jalingo a ranar Alhamis.

Ishaku ya ce ya tabbatar jami’an tsaro na bakin kokarinsu a jihar, don haka yana da tabbacin ’yan ta’addar ba su da wuri a jihar.

Kazalika, ya ce tuni ya sanar da masu sarautun gargajiya a jihar cewa su kasance masu sanya ido tare da bada rahoton ayyukan duk wasu bakin take-take ga jami’an tsaro.

Ya kara da cewa duk wadanda aka samu daga cikin masu sarautun gargajiyar ya saba umarnin, zai iya rasa rawaninsa.

“Binciken jami’an tsaro ya gano yadda ’yan ta’adda ke kokarin kafa sansani a Taraba, wannan aiki ne na masu sarautun gargajiyar da su sanar da duk wani motsi na wanda ba su yarda da shi ba,” a cewar gwamnan.

Har wa yau, ya jinjina wa Majalisar Dokokin jihar kan duba tare da amincewa da kasafin kudin cikin kankanin lokaci.

Darius Ishaku ya ba wa al’ummar jihar tabbacin cewa dukkanin ayyukan da ba a karasa ba, za a kammala su cikin shekara mai zuwa don su samu damar cin moriyarsu.