’Yan ta’adda na shirin kai hari Kano
’Yan sandan jihar sun buƙaci jama’a da su yi taka-tsan-tsan tare da kauce wa wuraren cunkoson jama’a har sai an bayar da sanarwa.
Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano ta sanar da jama’a kan wani shiri da ake zargin wasu ’yan ta’adda na kai hari a wuraren taruwar jama’a masu muhimmanci a faɗin jihar.
A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ’yan sandan jihar Abdullahi Kiyawa ya fitar, ya buƙaci jama’a da su yi taka-tsan-tsan tare da kauce wa wuraren cunkoson jama’a har sai an bayar da sanarwa.
- Dokar shara: Za a ci tarar masu gidajen mai dubu 200 – GOSEPA
- Za a hukunta iyayen da suka hana yara samun ilimi a Adamawa
Hakan zai ba jami’an tsaro damar ganowa tare da kawar da barazanar da ka iya tasowa.
“Rundunar ’yan sandan Jihar Kano tare da haɗin gwiwar wasu jami’an tsaro sun samu rahotannin sirri na wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne da ke shirin ƙaddamar da hare-hare kan taron jama’a a wurare masu muhimmanci a cikin Jihar Kano.
Sanarwar ta ƙara da cewa, “A saboda haka, muna kira ga mazauna yankin da su yi taka-tsan-tsan tare da kaucewa cunkoson wurare har sai an samu sanarwa a matsayin matakin kariya don bai wa jami’an tsaro damar gano matakan fatattakar maharan,” in ji sanarwar.
A cewar Kiyawa, rundunar ‘yan sandan ta tura ƙwararru daga sashen bama-bamai da sinadarai da masu nazarin halittu da jami’ai kan makaman nukiliya zuwa wasu muhimman wurare na jihar.
“Jami’an suna cikin shirin ko-ta-kwana kuma ana iya tuntuɓarsu ta 08169884988 ko 07067157218 don samun rahotannin mutanen da ake zargi ko abubuwan da ake zargi.