’Yan ta’adda na shirin kai harin bom a wuraren ibada —DSS

Gargadin nan zuwa ne bayan hare-haren bom da kungiyar ISWAP ta kai

’Yan ta’adda na shirin kai harin bom a wuraren ibada —DSS

Jami’in hukumar DSS

Hukumar Tsaro ta DDS ta yi gargadi cewa ’yan ta’adda na shirin kai hare-haren bom a wuraren ibada da wuraren shakatawa da sauran wuraren taruwar jama’a.

DSS ta ankarar da ’yan Najeriya cewa kungiyoyin ’yan ta’adda na kokarin yin hadin gwiwa domin kai hare-haren bom a wasu muhimman wurare a cikin Najeriya.

“DSS na sanar da jama’a game da shirin miyagu na mayar da Najeriya kamar yadda take kafin 2015 ta hanyar hare-haren bom a kan jama’a a sassan kasar,” inji hukumar.

Sanarwar daga kakakin DSS, Peter Afunanya, ta gargadi masu wuraren taruwar jama’a da masu gudanarwa da su dauki cikakkun matakan tsaro, domin kawar da duk wata batazanar tsaro a wuraren.

Afunanya ya ba da tabbacin cewa hukumar ta tashi haikan domin dakile shirin, kuma tuni jami’anta suka fara atisaye domin tabbatar da nasarar aikin na tsare rayukan al’umma.

“Saboda haka ana bukatar jama’a da su ci gaba da harkokinsu yadda suka saba, tare da jami’an tsaro duk wani motsin da ba su yarda da shi ba,” inji Afunanya.

Sabbin hare-haren bom

Wannan sanarwar ta DSS dai ba ta fayyace wadanda ake zargi da wannan mugun nufi ba.

Amma a baya-bayan nan kungiyar ISWAP ta kai hare-haren bom biyu a wasu mashaya biyu a Jihar Taraba, ta kashe akalla mutum 30, wasu kimanin 15 suka jikkata.

A safiyar Litinin an kashe ’yan sanda biyu a wani caji ofis da mayakan ISWAP suka kai wa hari a Karamar Hukumar Adavi ta Jihar Kogi.

A ranar Lahadi da dare, an samu rahoron harin bom da ake zargi a wata mashaya a garin Gashua, Jihar Yobe, inda aka tabbatar da mutuwar mutum daya.

Kawo yanzu dai babu wanda ya dauki nauyin harin na Gashua, wanda wasu majiyoyi ke cewa ba ’yan ta’adda ba ne.

A Jihar Borno ma mayakan sun kai hari kan wasu masu halarta bikin daurin aure da na nadin sarauta, inda suka bude wa mutane wuta.

A makon jiya ma, ISWAP ta kai hari a garin Geidam na Jihar Yobe, inda ta kashe mutum biyu a wata mashaya, bayan ta kona wata makarantar gwamnati a garin.

Za a iya tunawa a ranar 28 ga watan Maris, an kai harin bom a kan wani jirgin kasa da ke kan hanyarsa ta zuwa Kaduna daga Abuja, aka kashe mutum takswas tare da yin garkuwa da wasu.

Bayan harin dai ana ta kokwanto game da kasancewar maharan ’yan bindiga ko kuma ’yan Boko Haram.