’Yan ta’adda sun banka wa gida wuta masu gidan na ciki

A ranar Asabar da ta gabata ce wasu mutane da ba a san ko su wane ne ba suka banka wa gidan wani mai suna Aminu Ahmad Babale wuta inda suka yi sanadin mutuwar ’yarsa da kona wani dansa a Zariya Jihar Kaduna.Lamarin wanda ya faru a Uguwar Banzazzau a Jushi Zariya, mai gidan Malam […]

’Yan ta’adda sun banka wa gida wuta masu gidan na ciki

A ranar Asabar da ta gabata ce wasu mutane da ba a san ko su wane ne ba suka banka wa gidan wani mai suna Aminu Ahmad Babale wuta inda suka yi sanadin mutuwar ’yarsa da kona wani dansa a Zariya Jihar Kaduna.
Lamarin wanda ya faru a Uguwar Banzazzau a Jushi Zariya, mai gidan Malam Aminu, wanda babban gidansu ke Kwarbai ya shaida wa wakilinmu cewa bayan ya ce wa iyalansa da suke hira da misalin karfe 10:30 na dare cewa su je su kwanta, ya bude rediyo ke nan domin jin karatun da ake yi da karfe 11:00 sai amaryarsa ta zo rungume da yaro ta ce tana jin tafiya a bayan dakinta, kuma ana cikin haka ne shi ma ya ji tafiyar kamar ana ta guje-guje a tsakar gidan.
“Daga nan sai na kashe wutar dakina da na bayi sai na fara jin sun fara bugun gilasan taga da kofa can sai na ji ’yata ta yi kara sai matata ta firgita sai ta ce sun kama Bilkisu. Sai na ce ‘Inalillahi wa inna ilaihi raji’un,’ ita ma ta hau addu’a can sai na kara jin wata kara suna bugun kofa, daga nan na buga wa yayana waya na ce masa barayi sun shigo gidana kuma na buga wa wani yarona waya na ce ya tada makwabta, muna ta addu’a, ana cikin haka sai muka ji ana wuta-wuta. Sai matata ta ce a nan ne fa. Sai na ce mata a’a ba a nan ba ne, da abin ya tsananta kwarai sai na bude kofa, su kuma wadanda suka aikata hakan, da ma akwai wani durom da suka sa, sai suka haura ta baya,” inji shi.
Ya ce wutar ta yi sanadin kona ’ya’yansa biyu inda Bilkisu ta rasu, Abubakar Sadik ya kona yanzu haka yana kwance a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello. Ya ce duk kayan gidan sun kone babu abin da suka cire.
Malam Aminu wanda ya yi ritaya daga aiki shekara biyar da suka gabata, ya ce ba ya siyasa kuma babu wata matsala a tsakaninsa da wani, “don haka ban san abin da mutanen suke nufi ba,” inji shi.
Ya ce duk da bai kai rahoto ga jami’an tsaro ba sai dai wasu kwararru a kan tsaro daga barikin soja sun ziyarce shi sun yi masa tambayoyi sun kuma dauki hotunan gidan, kuma jami’an ba da agajin gaggawa sun je gidan.
Ya ce ya gode wa Allah da Ya tserr da rayuwarsu tare da takaita lamarin, kuma ya yi godiya ga jama’a da jami’an tsaro da na kashe gobara kan kokarin da suka yi wajen kashe gobarar. Ya roki gwamnati ta inganta harkokin tsaro, musamman samar wa jami’an tsaro da kayan aiki, “kuma ina ba da shawara a fitar da lambobin waya da jami’an tsaro a ba za su a ko’ina jama’a su samu yadda in wani abu na faruwa sai su sanar da su.