’Yan ta’adda sun bindige mutum 2 har lahira a Gwarzo
“Sama da mutane 500 na nan a wajen gari sun yi cirko-cirko. Akwai mutum uku da suka harba, suna Asibitin Gwarzo. Jimillar mutum huɗu dai suka harba,” in ji shi
Al’ummar garin Lakwaya da ke Ƙaramar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano, sun shiga firgici bayan ’yan bindiga sun kai musu hari, suka kashe mutum biyu, da raunata wasu huɗu.
Unguwannin da ’yan bindigar suka kai hari sun haɗa da Jajaye da Garin Mahauta, inda suka yi ya harbi kan mai uwa da wabi.
Kafar Premier Radio da ke Kano ta ruwaito cewa tun da misalin ƙarfe 5:00 na yamma ’yan ta’addan suka far wa garin, ana tsaka da cin kasuwa.
“Sun kora shanu da dama, waɗanda har zuwa yanzu ba a tantance adadinsu ba,” in ji wani mazaunin garin mai suna Malam Sani.
- Yawan mamata a harin jirgin soji a kasuwar Zamfara ya haura 150 —Shaidu
- Ɗan’iya ya zama ɗan takarar Gwamnan Sakkwato a ADC
Ya bayyana cewa harin mai tsauri ne fiye da na baya.v“Yanzu sun harbi mutum biyu. Sun zo Garin Mahauta inda suka taɓa zuwa suka kashe mutum ɗaya. Sai kuma garin Jajaye daf da gari sun kwashe shanun mutane.
“Sama da mutane 500 na nan a wajen gari sun yi cirko-cirko. Akwai mutum uku da suka harba, suna Asibitin Gwarzo. Jimillar mutum huɗu dai suka harba,” in ji shi.
A nasa ɓangaren ɗan Sarkin Lakwaya Yarima Sagir, ya ce sun samu rahoton cewa ’yan bindigar sun ɗana tarkonsu a ƙauyuka da dama na Gwarzo.
“Yanzu ake faɗa mana cewa sun ɗana tarkonsu a garuruwan Gandu da Garin Mahauta, da duk ƙauyukan nan na gefen Lakwaya.
“Sun kore wa mutane shanu kuma suna ta harbe-harbe. Jami’an tsaro sun fita yanzu an ce za su je su tunkare su,” in ji shi.
Wannan harin dai na daga cikin hare-hare da ’yan bindigar suka kawo jihar Kano daga Katsina, bayan ɗaukar lokaci ba a ji ɗuriyarsu ba.