’Yan ta’adda sun fara amfani da jirgi mara matuki —ONSA
Ofishin ya bayyana cewa ayyukan miyagun na barazana ga tsaro da kuma tattalin arzikin kasar
Ofishin Mai Ba Shugaban Kasa Shawara Kan Harkokin Tsaro ya bayyana damuwa bisa yadda ’yan ta’adda masu sauran masu aikata manyan laifuka ke amfani da jirage marasa matuka a Najeriya.
Ofishin ya bayyana cewa ayyukan miyagun na barazana ga tsaro da kuma tattalin arzikin kasar.
Amma ya bayyana cewa sun dauki matakai ta hannun Cibiyar yaki da ta’addanci da ke karkashinsa, da hadin gwiwar Gwamnatin Birtaniya domin shawo kan matsalar.
Shugaban Cibiyar, Manjo-Janar Adamu Laka, ne ya sanar da haka ranar Litinin a Abuja a wurin bude taron kara wa juna sani kan yaki da barazanar tsaro ta sararin samaniya (MANPADS).
- Sheikh Tijjani Guruntum ya gwangwaje dalibansa da kyautar kuɗi da kayan abinci
- Matatar Dangote: Minista na neman sasanta NNPC da Dangote
A cewarsa, “Wannan ya nuna muhimmancin mu yi aiki tare mu gano rawar da kowannemu zai taka domin samun gagarumar nasara a bangaren tsaro a sararin samaniyar kasar nan.
“Saboda haka ina hadin kanmu na da muhimmancin a wannan bangare tsakanin hukumomin cikin gida da ma na kasashen wajen magance wannan barazana, domin babu ruwansu da iyakokin kasashe.
“Shi ne dalilin cibiyar da ke karkashin ONSA (NCTC-ONSA) da hadin gwiwar Hukumar Tsaron Sufurin Jirage ta Birtaniya suke kokarin shawo kan lamarin a Najeriya a karshen wannan taro.
“yana da muhimmanci mu dauki wannan taro a matsayin matashiya domin samun nasara a kasar nan, nahiyar Afirka da ma duniya,” in ji shi.
A cewarsa, ya zama wajibi mahalarta taron su yi duk mai yiwuwa domin shawo kan lamarin.
A nasa bangaren, Mista Jonathan Kendall daga Birtaniya, ya ce taron zai mayar da hankali ne kan magance matsalar.
Kendall ya bayyana cewa “mun kawo dakarun sojin Birtaniya da suka kware a yaki da ta’addanci a wannan banagre, domin taimaka wa Najeriya ta samu karfi da fasahar da ake bukata domin iya dakile barazanar da wuri.