’Yan ta’adda sun ga harbi likita sace wasu a asibiti a Katsina

’Yan ta’adda sun buɗe wa likitan wuta sannan suka yi awon gaba da ma’aikatan lafiya a Babban Asibitin Ƙanƙara da ke Jihar Katsina

’Yan ta’adda sun ga harbi likita sace wasu a asibiti a Katsina

Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umaru Radda. (Hoto: Gwamnatin Jihar Katsina).

Wani likita sun tsallake rijiya da baya da raunukan harbi bayan ’yan bindiga sun buɗe masa wuta a asibiti a Jihar Kastina.

A ranar Talata ne ’yan ta’addan suka kutsa cikin Babban Asibitin Ƙanƙara da ke Ƙaramar Hukumar Ƙanƙara suka yi awon gaba da ma’aikatan lafiya da ba a kai ga tantance yawansu ba.

Wani shaida ya bayyana cewa ’yan bindigar sun harbi likitan a ƙafa, amma ya sha da ƙyar, kuma a halin yanzu yana samun kulawa a wani wuri da ba a bayyana ba.

Mazauna yankin sun bayyana cewa da shigar maharan harabar asibitin suka fara ɓarin wuta kan mai uwa da wabi, inda suka tayar da hankalin kowa.

Kakakin ’yan sanda a Jihar Katsina, ASP Abubakar Sadiq Aliyu, ya gaskata faruwar lamarin amma ya shaida wa wakilinmu cewa daga baya zai yi ƙarin bayani.