’Yan ta’adda sun guntule hannun wani bebe a Kano
A safiyar ranar Lahadin da ta gabata ne wasu ’yan ta’adda suka guntule hannun wani bebe mai suna Salisu Garba a Unguwar Marmara a karamar Hukumar Birnin Kano.Lamarin ya faru ne a tsakiyar dare lokacin da Salisu Maitama Garba wanda yake suyar doya da kwai yake barci a soron gidansu inda masu aika-aikar wadanda ba […]
A safiyar ranar Lahadin da ta gabata ne wasu ’yan ta’adda suka guntule hannun wani bebe mai suna Salisu Garba a Unguwar Marmara a karamar Hukumar Birnin Kano.
Lamarin ya faru ne a tsakiyar dare lokacin da Salisu Maitama Garba wanda yake suyar doya da kwai yake barci a soron gidansu inda masu aika-aikar wadanda ba a san ko su wane ne ba suka bi dare suka sassare shi a kansa da fuskarsa sannan suka yanke masa hannu.
Umar Ahmad da ak fi sani da Mamili da suke gida daya da beben ya shaida wa Aminiya cewa ba su san abin da ya faru ba, sai da suka fito da safe suka samu beben a sume cikin jini, inda daga nan suka dauke shi zuwa asibiti. “Babu wanda ya ji lokacin da masu aika-aikar suka yi wannan mugunta a kansa da yake
bebe ne ko ya yi ihu babu wanda zai ji. Sai da gari ya waye muka fito muka ga hannunsa a gefe, shi kuma ya suma yana kwance cikin jini male-male. Daga nan muka sanar da ’yan sanda aka dauke shi zuwa Asibitin Murtala,” inji shi.
Wani mkwabcinsu mai suna Bashir Aminu Garba ya shaida wa Aminiya cewa “Da muka tashi da safe ne
muka samu labarin abin da ya faru. Nan da nan muka je kofar gidan inda muka ga hannun beben a kasa kuma duk fuskarsa a kumbure saboda sarar da aka yi da wuka. Jini kuwa a wurin kamar an yanka rago.”
’Yan uwan beben sun ce a iya saninsu bai yi fada da kowa ba, amma ba su sani ba ko ya bata wa wani rai ta hanyar kasuwancinsa, kuma ya dauki wannan mummunan mataki a kansa.
Kakakin Rundunar ‘Yan sandan Jihar Kano DSP Magaji Musa Majiya ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce sun kai beben asibiti inda yake jinya, kuma ya ce suna nan suna bincike don gano wadanda suka yi wannan danyen aiki don su fuskanci hukunci.