‘Yan ta’adda sun hallaka sojojin Burkina Faso 53
Gwamnatin sojin Burkina Faso ta ce sojojinta 17 da wasu jami’an sa-kai 36 sun rasu a wata gagarumar arangama tsakaninsu da ‘yan ta’adda
Gwamnatin sojin Burkina Faso ta sanar da mutuwar sojojinta 17 da wasu jami’an sa-kai 36 a wata gagarumar arangama tsakanin ‘yan ta’adda da jami’an tsaro.
A wata sanarwa da gwamnatin ta fitar tace ‘yan ta’addar sun farwa sojojin ne a kauyen Yatenga, inda sojojin ke aikin tabbatar da tsaro kuma ba tare da bata lokaci ba suka bude musu wuta.
- DAGA LARABA: Me Ya Sa Juyin Mulki A Wasu Kasashe Ya Dami Tinubu?
- Kungiyar Tsakiyar Afrika ta kori Gabon daga cikin mambobinta
Sanarwar ta kuma kara da cewa duk da sojojin sun mayar da martani, amma kuma wutar ta yi tsananin da sai da ‘yan ta’addar suka hallaka sojojin 17.
Burkina Faso ta kasance cikin kasashen yankin Sahel da ke fama da ayyukan ta’adda tun 2015, lokacin da mambobin kungiyar Al-Qaeeda suka fara kai munanan hare-hare a sassan kasar.
Bayanai sun nuna cewa hare-hare sun tsananta a kasar tun bara, duk kuwa da yadda sojojin ke ikirarin tabbatar da tsaro bayan karbe iko daga hannun farar hula.
Ko a lokacin da ‘yan kasar ke zanga-zangar nuna goyon bayan su ga sojoji an ga yadda suka rika daga tutar kasar Rasha, da kuma kira kan ta kaiwa kasar dauki ta fannin yaki da ta’addanci.