’Yan ta’adda sun harbi shugaban rundunar tsaron al’ummar Zamfara
’Yan bindiga sun harbi Janar Lawal B. Muhammad, wanda a shi ne Darakta-Janar na Rundunar Taron Al’umma ta Jihar Zamfara.
Janar Lawal B. Muhammad, Darakta-Janar na Rundunar Taron Al’umma ta Jihar Zamfara ya tsallake rijiya da baya a hannun ’yan bindiga.
’Yan ta’addan sun harbi Janar Lawal ne a yayin harin da suka kai kauyen Kucheri da ke Ƙaramar Hukumar Tsafe ta jihar.
Wani jami’in hukumar ya tabbatar mana cewa, “Gaskiya ne ’yan bindiga sun karbi Darakta-Janar na Rundunar Tsaron Al’umma ta Jihar Zamfara, a kwankwasonsa, amma yana samun kulawa a Asibitin Ƙwararru na Yariman Hakura da ke Gusau,” bayan faruwar lamarin.
A yammacin ranar Asabar ne suka tare babbar hanyar Funtua-Tsafe inda suka riƙa kai wa mahara hari, ciki har da Janar Lawal Murabus.
- Yadda mayaƙan Hamas suka shafe sa’a 6 suna kai hari a Isra’ila
- Zaɓen ƙananan hukumomi: Wainar da ake toyawa a jihohi
Aminiya ta gano cewa maharan sun yi masa mummunan rauni sakamakon harbin sa da suka yi a kwankwaso a yayin harin.
’Yan ta’addan sun kuma yi abin gaba da wasu matafiya da dama a yayin harin.