’Yan ta’adda sun kashe Likita da Hakimi a Bauchi

Wasu ’yan ta’adda da ba a san ko su wane ne ba sun kashe Shugaban Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya dake Azare a Jihar Bauchi, Dokta Musa Mohammed Dambam da Hakimin Yamai, Alhaji Manu Abubakar Yamai, a ranar Asabar da ta gabata.Dokta Dambam yana kan hanyarsa ta zuwa Azare ne daga Dambam tare da kanwar […]

’Yan ta’adda sun kashe Likita da Hakimi a Bauchi

Marigayi Dokta Musa DambamWasu ’yan ta’adda da ba a san ko su wane ne ba sun kashe Shugaban Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya dake Azare a Jihar Bauchi, Dokta Musa Mohammed Dambam da Hakimin Yamai, Alhaji Manu Abubakar Yamai, a ranar Asabar da ta gabata.
Dokta Dambam yana kan hanyarsa ta zuwa Azare ne daga Dambam tare da kanwar mahaifiyarsa mai suna Hajiya A’isha Daguji Adamu da zai kai ta Bulkachuwa don ta wuce Hardawa.
Hajiya A’isha ta ce mutum uku sanye da kakin soja ne suka tare su, inda mutum na farko ya leka motar sai ya ce shi ne, daga nan suka ce ya koma kujerar baya inda take zaune.
Ta ce bayan sun karbi katin shaidar aikinsa da takardu da kudinsa, sai daya ya tuka motar daya ya zauna a baya tare da su, suka nufi garin Yamai kimanin kilomita 10 daga Dambam.
Hajiya Daguji ta ce sun isa garin Yamai da misalin karfe 8:00 na dare, inda aka fitar da su aka zaunar, aka bar mutum biyu suna gadinsu daya ya koma da motar don dauko sauran abokan tafiyarsu su uku. “Nan muka zauna har zuwa karfe 10:15 na dare,” inji ta.
Ta ce mutanen suna zuwa suka dauke shi suka tafi suka bar ta, ta ce da su yaya za su tafi su bar ta, suka ce suna dawowa za su je aiki ne.
daya daga cikin matan Hakimin Yamai mai suna Adda Binta ta ce a lokacin da suka shiga gidan sun fito da shi suka ce ya kawo kudi kuma ya umarci dukkan matan gidan su kawo kudin da ke hannunsu. Ta ce sun ce idan suka sake binciki gidan suka samu kudi za su kashe su, daga nan suka dauke hakimin da niyyar zuwa gidan wakilinsa a kan hanya suka harbe shi suka tafi. Hajiya Daguji ta ce da Asuba ne aka shaida mata an kashe dan nata.
An yi jana’izar Dokta Musa a ranar Lahadi a Dambam, yayin da aka yi jana’izar Sarkin Yamai a garin Yamai.
Dokta Musa Dambam mai shekara 55 wanda ya rasu ya bar mace daya da ’ya’ya bakwai, mutum ne mai saukin kai da son ci gaban jama’a.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Bauchi ASP Hassan Mohammed Auyo ya ce suna ci gaba da bincike don gano makasan, kuma ana samun ci gaba game da binciken da ake yi, don haka ya nemi jama’a su taimaka musu da bayanan dukkan mutanen da ba su yarda da take-takensu ba a yankin.