’Yan ta’adda sun kashe manyan hafsoshin soji 6 a Chadi

Janar Youssouf Abdoulaye Kari, wanda tsohon mamba ne na rundunar sojojin Chadi a Mali, na daga cikin waɗanda aka kashe.

’Yan ta’adda sun kashe manyan hafsoshin soji 6 a Chadi

Rahotanni sun bayyana cewar aƙalla manyan hafsoshin soji shida na Jamhuriyar Chadi sun rasa rayukansu, tare da jikkatar wasu da dama a wani harin kwanton ɓauna da ’yan ta’addar Boko Haram suka kai wa sojojin ƙasar a gaɓar Tafkin Chadi.

Ƙwararren mai sharhi kan yaƙi da tayar da ƙayar baya a yankin Tafkin Chadi, Zagazola Makama, ’yan ta’addan na Boko Haram sun aiwatar da wannan hari ne a ranar Juma’a, 8 ga watan Nuwamba.

Makama ya ce har na zuwa jim kaɗan bayan Shugaban Kasa Mahamat Idriss Deby ya tashi daga yankin domin komawa babban birnin kasar, Ndjamena.

Daga cikin waɗanda suka rasu akwai manyan hafsoshin kasar da suka haɗa da Janar Youssouf Abdoulaye Kari, Janar Adoum Issa, Kanar Lony Allatchi, Laftanar Kanar Gorou Wardougou, Adam Nassour Mahamat, da Idrissa Malloum.

Har ila yau harin ya yi sanadin raunata wasu manyan Hafsoshinn sojoji, kamar Janar François Tatiko, Janar Moubarack Formalick, Bokhit Bachar, Laftanar Jean Pierre Medar, da Ibrahim Ali.

Janar Youssouf Abdoulaye Kari, tsohon sojan da ake mutuntawa, kuma tsohon mamba ne na rundunar sojojin Chadi a Mali, na daga cikin waɗanda aka kashe, wanda ya bar baya da kura a shugabancin soja.

Kazalika, kakakin rundunar sojin ƙasar Chadi, Janar Issakha Acheikh ya fitar da sanarwa dangane da wannan harin na kwantan ɓauna da aka yi wa sojojin ƙasar amma bai yi wani ƙarin bayani ba.

Zagazola ya ambato Babban Hafsan Sojin ƙasar yana cewa tuni an yi garambawul ga rundunar OPERATION Haskanite da aka ba da umarnin ƙaddamar da shirin fatattakar ‘yan ta’addar Boko Haram daga Tafkin Chadi, inda har sun yi artabu na farko a ranar, Asabar 09 ga watan Nuwamba, 2024.

Ya yi bayanin cewa, bayan shafe sa’o’i kaɗan ana gwabzawa, an kashe ‘yan ta’addan da dama, kuma an ci gaba da kai farmakin yayin da ya ƙara da cewa nan gaba za a sanar da ƙarin bayani.