’Yan ta’adda sun kashe mutum 10 a kasuwa a Katsina

Wata mai juna biyu tana cikin mutanen da aka kashe, kuma maharan sun kona gidaje da dama tare da sace dabbobi da ba san adadinsu ba

’Yan ta’adda sun kashe mutum 10 a kasuwa a Katsina

’Yan ta’adda sun bindige akalla mutane 10 har lahira a yayin da ake tsaka da cin kasuwa a Kasuwar Hatsi da ke kauyen Guga a Karamar Hukumar Bakori ta Jihar Katsina.

Rahotanni sun bayyana cewa wata mai juna biyu tana cikin mutanen da maharan suka kashe, kuma sun kone gidaje da dama tare da sace dabbobi — shanu da awaki da tumaki, da ba kai ga  gano adadinsu ba,.

“Sun kona gidaje sun sace kaya. Sun fasa daruruwan shaguna  sun sace kayayyakin ciki a kasuwar,” a cewar wata majiya a kauyen Guga.

Shaidu sun ce maharan sun kai farmakin ne da rana tsaka, inda suka yi ta harbi kan mai wuwa da wabi, kuma sun dauki lokaci suna cin karensu babu babbaka.

Wani shaida ya bayyana cewa, “Sun kashe wata mata da ta zo yin sayayya a kayan abinci a kasuwar, inda suka rika harbe-harbe ta kowace kusurwa. Dole mutane suka yi ta tserewa.

“Sun dauki lokaci suna cin karensu babu babbaka ba tare da sun fuskanci wata turjiya ba, suka karkashe mutane tare da kwashe kayayyaki a shaguna kafin su tafi.”

Mazauna garin sun ce an yi jana’izar mamatan ne a safiyar Litinin a kauyen Guga, kuma “yawancinsu mamatam sun zo ne daga kauyuka makwabta — Gidan Sarkin Noma and Gidan Wawu. Manoma ne da suka zo su sayar da amfanin gonakinsu.”

Kauyen Guga ya sha fama da hare-haren ta’addanci da garkuwa da mutane, wadanda a baya suka sa da dama cikin mazauya yankin gudun hijira.

“Mun gaji da binne ’yan uwanmu, domin ba wannan ne karon farko da suka kawo mana irin wannan hari ba. Muna bukatar mafita mai dorewa,” in ji al’ummar yankin,” in ji shi

Al’ummar yankin sun  bukaci hukumomi da su sake farfado da tattaunawar sulhu da aka yi da tubabbun ’yan ta’adda domin kara inganta tsarin tsaron al’ummomi.

Kazalika sun roki Gwamnatin Tarayya da ta Jihar Katsinsa da su kara hadin gwiwa domin magance karuwar matsalolin tsaro a yankin.

Wakilinmu ya yi  kokarin samun karin bayani game da harin daga hukumomin tsaro amma abin ya gagara.

Ya yi magana da kakakin ’yan sanda na jihar, wanda ya ba shi tabbacin cewa zai binciki halin da ake ciki kafin ya yi bayani, amma har zuwa lokacin da muka kammala hada wannan labarin hakan bai samu ba.