’Yan ta’adda sun kashe wani babban limami a Borno

A watan da ya gabata ne mahara suka kashe kanin babban limami a Borno.

’Yan ta’adda sun kashe wani babban limami a Borno

Mahara

Mayakan Boko Haram sun kashe babban limamin garin Beneshiekh da ke Karamar Hukumar Kaga a Jihar Borno, Sheihk Baba Goni Muktar Malumti.

Lamarin ya auku ne yayin da ’yan ta’addan suka kai farmaki da safiyar Litinin din da ta gabata, inda kuma suka kona wasu littattafan karatu na marigayin.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da wasu gungun ’yan ta’adda suka kai farmaki kauyen Makinta Kururi na Beneshiekh, inda suka yi awon gaba da mafarauta biyu.

Ana iya tuna cewa, a watan da ya gabata ne mahara suka kashe kanin babban limamin yayin wani farmaki da suka kai kauyen na Makinta.

Kantoman Karamar Hukumar Kaga, Hon Mustapha Bukar Baima ya tabbatar da faruwar lamarin a wata tattaunawa ta musamman da manema labarai ranar Litinin a Maiduguri.

Ya bayyana kaduwarsa kan sabbin hare-haren da ‘yan ta’adda suke yi wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da dama, musamman kisan gillar da aka yi wa babban limamin Beneshiekh da kuma sace mafarauta biyu a yankin.

“Eh, mun samu kiran gaggawa cewa ‘yan ta’addan Boko Haram sun bindige babban limamin masallacin Juma’a na Beneshiekh a gidansa da misalin karfe 1:15 na wayewar garin Litinin.

“’Yan ta’addan sun fara kai farmaki gidan wani Malamin addinin Musulunci, amma da suka fahimci hoton da suke dauke da shi domin aiwatar da hukuncin kisa bai kama da na babban Limamin da aka kai masa hari ba, sai suka ce ya koma gidansa ya zauna.

“Bayan nan suka je wani gida, inda babban Limamin yake daga nan ne ‘yan ta’addan suka bude masa wuta bayan da suka fahimci cewa hoton da suke dauke da shi ya yi daidai da wanda za su cika aiki a kansa.

“Yan ta’addan sun kuma kona wasu Littattafan Musulunci bayan sun kashe babban Limamin wanda tunin aka yi jana’izar sa a ranar ta Litinin a garin na Benesheik kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

“Mun samu rahoton cewa wasu ‘yan ta’addan sun kai mamaya Makinta Kururi, inda suka yi awon gaba da mafarauta biyu.

“Ina so in yi ta’aziyya ga iyalan mamacin, kuma Allah Ya ba marigayin Jannatul Firdausi,” a cewar Hon Baima.

Baima ya ce sun sanar da hukumomin soji game da hare-haren da suka auku, kuma a halin yanzu suna bin sahun ‘yan ta’addan domin daukar matakin da ya dace.

Garin Beneshiekh na da nisan kilomita 70 daga Maiduguri kuma yana kan babbar hanyar Kano zuwa Damaturu.