’Yan ta’adda sun kona gonaki 6 kafin a girbe abincin da aka noma a Kaduna

Manomin ya ce bara ya samu buhu 160 na masara a gonar kuma yana sa ran samun fiye da haka a bana, amma kafin ya girbe ’yan fashin daji suka kona gonar da wasu biyar a yankin Birnin Gwari a Jihar Kaduna.

’Yan ta’adda sun kona gonaki 6 kafin a girbe abincin da aka noma a Kaduna

Gonar Masara

’Yan fashin daji sun kona wasu gonakin masarar shida kafin a girbe su a kauyukan Kwaga da Unguwar Zako da ke Karamar Hukumar Birnin Gwari a Jihar Kaduna.

Danyen aikin ’yan ta’addan ya girgiza al’ummar kauyukan, musamman masu gonakin da abin ya shafa, inda suka rika nuna alhini.

Wakilinmu ya ga bidiyon irin barnar da wutar da ’yan fashin dajin suka cinna ta yi a gonakin.

Daya daga cikin masu gonakin, Malam Kabiru Halilu Kwaga, ya shaida wa Aminiya cewa a bara ya noma buhu 160 na masara a gonar, kuma a bana yana kyautata zaton samun fiye da haka, amma maharan suka kona gonar.

Malam Surajo Kwaga kuma ya ce buhu 40 ya samu a gonar bara, amma bana an kone ta dungurungum.

Shi kuma Malam Dan Gido, da ya samu buhu 50 a bara, ya ce ya yi fatan samun kimanin buhu 65 a gonar a bana, amma kuma wannan abin ya faru.

Malam Jibril Kwaga da ya rasa amfanin gonarsa a wannan mummunan hari ya yi fatan Allah Ya mayar musu da mafi alheri.

Da yake tabbatar da lamarin, Shugaban Kungiyar Masu Kishin Yankunan Birnin Gwari da ke Makwabtaka da Jihar Neja, Ishaq Usman Kasai, ya yi zargin cewa ’yan fashin dajin da suka kona gonakin, yaran dan ta’adda Yellow Jamburos ne, da suke addabar yankin.

Wakilinmu ya yi kokarin samun karin bayani daga kakakin rundunar ’yan sanda na Jihar Kaduna, ASP Mansir Hassan, amma ya kasa samun jami’in a waya, har zuwa lokacin da muka kammala wannan labari.

Bin diddigi: Gaskiyar batun kai hari a Bankin CBN

NAJERIYA A YAU: Lakurawa muka kai wa hari a Sakkwato —Sojoji

Manyan alhinin Najeriya a 2024

’Yan sanda sun kama waɗanda suka shirya rikicin ‘yan daba a Kano