’Yan ta’adda sun sace mutane a Fadar Sarki a Kwara

Maharan sun kona fadar sarkin sannan suka kai hari a ofishin ’yan sanda, washegarin da aka kashe masu ibadar dare uku tare da yin garkuwa da wasu 15

’Yan ta’adda sun sace mutane a Fadar Sarki a Kwara

’Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane kimanin 10, ciki har da mata da kananan yara a harin da suka kai fadar Sarkin Yashikira, da ke ke Karamar Hukumar Baruten ta Jihar Kwara.

Rahotanni sun bayyana cewa  a a cikin daren ranar Lahadi ne mahara dauke da muggan makamai suka kai harin, inda suka rika harbi babu kakkautawa, maharan suka kona fadar sarkin.

Mazauna yankin sun bayyana cewa maharan sun dauki awanni suna cin karensu babu babbaka ba tare da wata turjiya ba.

Majiyoyi sun ce bayan harin wanda ya zo wa al’ummar yankin da ba zata, jami’an tsaro sun fara aikin kokarin ceto wadanda aka yi garkuwa da su.

A cewarsu, sojoji da ’yan sanda sun fara shara a dazukan da ke yankin da zummar ceto mutanen da aka sace.

Sun bayyana cewa maharan sun kai hari a ofishin ’yan sanda da ke yankin, amma jami’an da ke bakin aiki suka fatattake su, bayan musayar wuta.

Wannan lamari ya faru ne washegarin da ’yan bindiga suka kai wa masu ibadar dare hari yankin Ori-Oke Ajaiye, da ke wajen kauyen Ikiran a Karamar Hukumar Ekiti ta Jihar Kwara, inda suka kashe mutum uku tare da yin garkuwa da wasu 15.