’Yan ta’adda sun shiga kone motocin jama’a a Kano
Al’ummar unguwar Gwauron Dutse da ke birnin Kano sun nemi Gwamnatin Jihar Kano ta kai musu dauki bisa halin da suka shiga inda yadda wasu ’yan ta’adda ke amfani da yanayin sanyin da ake ciki suna kone musu motoci. Rahotanni sun bayyana cewa ’yan ta’adar wadanda ba a san ko su wane ne ba, sun […]

Al’ummar unguwar Gwauron Dutse da ke birnin Kano sun nemi Gwamnatin Jihar Kano ta kai musu dauki bisa halin da suka shiga inda yadda wasu ’yan ta’adda ke amfani da yanayin sanyin da ake ciki suna kone musu motoci.
Rahotanni sun bayyana cewa ’yan ta’adar wadanda ba a san ko su wane ne ba, sun fara wannan ta’addaci ne a ranar Juma’ar da ta gabata, inda suka kone motoci bakwai a Layin Bayan Reka da ke unguwar sannan a ranar Lahadi suka kuma kone wasu motoci shida a gidan man URAMCO da ke unguwar.
Aminiya ta gano cewa kafin ’yan ta’adar su kone motocin sai da suka yi artabu da maigadin gidan man, wanda a karshe suka yanke shi da wuka a hannunsa.
Malam Garba AP shi ne maigadin gidan man URAMCO, ya shaida wa Aminiya cewa da misalin karfe 3:00 na dare yana kwance sai ya ji motsin mutane a cikin gidan man. Hakan ya sa ya tashi ya tunkare su. “Bayan na ga wani matashi ya tsallaka titi sai na bi shi, inda muka kama kokawa da shi, sai dai duk ban iya gane fuskarsa ba. A nan dai ya sa wuka ya yanke ni sannan ya gudu ya bar ni a wurin a kwance.
Daga nan sai na tashi na dawo gidan man inda na tarar motoci uku da ke ajiye a gidan man suna cin wuta. Nan da nan sai na fasa gilashin ofishin manaja na dauko abin kashe wuta na hau fesa wa motocin. Hakan ya sa wutar ta tsagaita da ci. To ashe bayan sun bar gidan manmu sun tsallaka daya gefen, a can ma sun kone wasu motocin uku,” inji shi.
daya daga cikin wadanda ’yan ta’addan suka kone wa motocin Alhaji Ibrahim Abdullahi ya bayyana wa Aminiya cewa ba su zargin wasu da alhakin faruwar wanann lamari ba, sai dai suna kira ga gwamnati da ta ribanya kokarinta wajen tsaron da take bayarwa ga jama’a.
Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano, DSP Magaji Musa Majiya ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce tuni rundunarsu ta shiga bincike don gano wadanda ke da hannu a cikin wannan aika-aika.