’Yan ta’adda sun tsere daga gidan yarin Nijar
Fursunoni da dama sun tsere daga gidan yarin garin garin Koutoukale inda ake tsare da manyan mayakan jihadi
Manyan ’yan ta’adda sun tsere daga babban gidan yarin garin Koutoukale a Jihar Tillabery da ke Jamhuriyar Nijar.
Hukumomin Nijar sun ayyana dokar hana zirga-zirag a fadin Jihar Tillabery sakamakokn tserewar fursunonin.
Ma’aikatar Harkokin Cikin Gidan kasar ta tabbatar da tserewar fursunoni da dama ciki har da manyan ’yan ta’adda daga gidan yarin.
A ranar Alhamis da fare ne fursunonin suka tsere bayan fasa gidan yarin da ke garin Koutoukale mai nisan kilomita 50 daga binin Niamey.
- Makaranta ta rushe da dalibai suna zana jarabawa a Jos
- Kudin tashar Mambilla: An ba da belin tsohon ministan lantarki kan N10bn
A baya a sau biyu a shekarun 2016 da 2019 fursunoni sun yi yunkuri tserewa daga gidan yarin amma jami’an tsaro na dakile su.