’Yan ta’adda sun sace dalibai 25 a dakunan kwanansu a Kebbi

’Yan sanda sun bayyana cewa maharan sun bindige MataimakiN Firinsifal din makarantar a lokacin da yake kokarin hana ’yan bindigar tafiya da daliban

’Yan ta’adda sun sace dalibai 25 a dakunan kwanansu a Kebbi

Taswirar Jihar Kebbi

’Yan ta’adda sun harbe Mataimakin Firinsifal har lahira, sa’annan suka yi garkuwa da dalibai 25 a dakunan kwanansu a Makarantar ’Yan Mata ta Gwamnati (GGCSS) da ke yankin Maga a Karamar Hukumar Danko Wasagu ta jihar Kebbi.

Mazauna yankin sun bayyana cewa maharan sun bindige Malam Hassan Yakubu Makuku ne a yayin da yake kokarin kare daliban, a lokacin farmakin da aka kai makarantar da misalin karfe 5.20 na Asubahin ranar Litinin.

Wani shaida ya ce, “Harin ya dimauta al’ummar garin Maga, yanzu muna cikin zullumi da alhini.” Ya kara da cewa, ’yan ta’addan sun harbe Malam Hassan ne a yayin da yake kokarin hana su tafiya da daliban.”

Kakakin ’Yan Sanda a Jihar Kebbi, CSP Nafiu Abubakar, ya shaida wa Aminiya cewa ’yan ta ’adda dauke da muggan makamai sun far wa yankin ne suna harbi kan mai uwa da wabi, kafin su tsallaka katangar makarantar su  su sace dalibai 25.

A cewarsa, “tawagar ’yan sanda ta musamman ta isa wurin inda ta yi musayar wuta da ’yan ta’addan, amma an yi rashin sa’a ’yan ta’addan sun sace daliban daga dakunan kwanansu”

Wani mazaunin garin Maga, Aliyu Yakubu ya ce ’yan ta’addan sun kutsa cikin makaratar ba tare da fuskantar wata turjiya ba.