‘Yan ta’adda suna fakewa da Musulunci ne kawai – Dokta Bilal Philips

Dokta Abu Ameenah Bilal Philips, Muslimin kasar Kanada ne da ke zaune a kasar katar yana yada ilimin addinin Musulunci, inda ya shahara da wa’azi a tashohin tauraron dan Adam. A makon da ya wuce malamin ya zo Najeriya, bayan da ya samu gayyatar wata kungiyar Musulunci ta Light of the Umma. Wakilan Aminiya sun […]

‘Yan ta’adda suna fakewa da Musulunci ne kawai – Dokta Bilal Philips
‘Yan ta’adda suna fakewa da Musulunci ne kawai – Dokta Bilal Philips

 Dokta Bilal Philips

Dokta Abu Ameenah Bilal Philips, Muslimin kasar Kanada ne da ke zaune a kasar katar yana yada ilimin addinin Musulunci, inda ya shahara da wa’azi a tashohin tauraron dan Adam. A makon da ya wuce malamin ya zo Najeriya, bayan da ya samu gayyatar wata kungiyar Musulunci ta Light of the Umma. Wakilan Aminiya sun gana da shi lokacin day a ziyarci kamfaninmu, inda ya yi bayani kan matsalolin da suka shafi ta’addanci da inshorar Musulunci ta Takaful. Ga dai yadda hirar ta kasance:

Aminiya: A Najeriya muna fama da matsalolin da suka hada da garkuwa da mutane da daba ko bangar siyasa. Shin ko akwai wasu dabaru na Musdulunci da za su magance wadannan munanan dabi’u?
Dokta Bilal: A gaskiya ba komai zan ce na sani ba game da al’ummar Najeriya, amma idan aka yi maganar matsalolin zamantakewa ko illolin da ke addabar al’umma, ina ganin al’amari ne da ya ta;’allaka a kan shugabanci. Idan aka samu jagoranci nagari, al’umma za ta kasance cikin managartan dabi’u. Da yake Riyadh na sani (a kasar Saudiyya), inda na shafe shekara 20, ban san wani da aka sace aka yi garkuwa da shi ba. Kuma mutane da dama sun zauna a birnin Riyadh tsawon shekara 40  ba su san wannan matsalar ba. Don haka ban taba kulle kofar gidana  ba; ko kulle motata idan na aje ta ba. Ban taba shiga cikin damuwa kan cewa ko wani zai sace mini mota ba. Ba a taba haura mini gida ba; ban kuma san wani da aka haura wa gida ba. Tun da irin wadannan al’amura ba su faru ba; ba a rubuta labarinsu a jarida ba, an samu kariyar rayuwa da zaman lafiya. Al’umma ta samu kariya da zaman lumana. Sai mu tambayi kanmu, daga ina aka samu wannan? Me ya sa ba a samun irin wannan a ko’ina? Ina ganin dalilin hakan bai rasa nasaba da aiwatar da shari’ar Musulunci a daukaci fadin kasar, al’amarin da ya ta’allaka da shawo kan rashin adalci. Kuma tsarin da yake daidai a mike, don haka ba a cika yi masa tawili barkatai ba. Wannan tsari dai nagartarsa ta tabbata tsawon shekara fiye da 1400, don haka shi ne tsarin tafiyar da al’umma mafi inganci ga Musulmi. Ina da tabbbacin cewa shi ne mafi kyawun tsari ga kowace irin al’umma. Sai dai akwai mahangar fahimta da yawa, don haka bai kamata a tursasa kowane irin mutum kan cewa sai ya bi koyarwa ta shari’a ba. Kodayake ga al’ummar Musulmi idan suka fi yawa hakkinsu ne su aiwatar da tsarin (shari’a). Kuma ba yana nufin ta’addanci ba ne ; ko kunar bakin wake da tsattsauran ra’ayi da makamantansu ba, al’amuran da a halin yanzu ake kokarin alakanta su da shari’a. Kai ta kai ga cewa, jihohi 22 daga cikin 52 na Amurka sun ce sun haramta shari’a, sai mutane suka bijiro da tambaya kan cewa mene ne aka hana? Amsar ita ce,  ‘mun hana kunar bakin wake,’ amma sai aka nusar da su cewa, wannan ba shari’a ba ce, kuma a irin fahimtarsu shari’a na nufin tashin hankali. Sai dai shari’a na nufin sallah sau biyar  a rana, raba zakka daga dukiyar mawadata ga talakawa. A tsarin duniya na hukunta masu aikata miyagun laifuka ya kauce wa hukuncin kisa, inda suke nuni da cewa kisan wanda ya kashe wani ba zai dawo da rai na wanda aka kashe ba. Sai dai ba a san cewa, illar da za ta auku a sanadiyyar rashin aiwatar da kisan na iya haifar da wani kisan.
Kai ta kai ga a kasar Birtaniya ana ta gina kurkuku, har sai da aka mayar da wani katon tsohon jirgin ruwa ya zama kurkuku. Abin da za a iya fahimta a nan shi ne duk sa’adda hukuma ta ki aiwatar da hukunci na adalci za ta kare da gina kurkuku. Shi ya sa ma zan iya kididdige yawan yanke hannu da na taba gni an yi na haddi a Saudiyya, tsawon shekara 20 da na zauna. Kuma manufar haddi ita ce kawai a kange mutum daga aikata barna, ta yadda mai yunkurin aikata laifin sata zai san cewa, akwai yiwuwar ya rasa hannunsa.

Aminiya: kokarin kafa daular Musuunci da yin aiki da shari’a shi ake alakantawa da kungiyoyi na ISIS da Boko Haram da makamantansu. Ko za ka yi mana karin haske?
Dokta Bilal: Tsattsauran ra’ayin addini al’amari ne da ya wanzu a daukacin al’ummomi tsawon tarihin  ci gaban rayuwar dan Adam. An sha samun matsalolin tsattsauran ra’ayin addini a kusan ko’ina. Ba wani sabon al’amari ba ne; ba kuma Musulunci kadai ke fama da wannan matsalar ba. Wannan matsalar kafafen yada labarai ne ke danganta Musulunci da tsattsauran ra’ayi. Idan kana karanta jaridu akwai yiwuwar a samu labarin tsatttsauran ra’ayin addini a Kirastanci, amma ba a taba danganta shi da tsattsauran ra’ayi ba. Don haka kodayaushe ake son nuna Musulmi shi ne mai tsattsauran ra’ayi ko Musulunci addinin tsauri ne. An sha jin irin wadannan kalaman, har ta kai ga an gina tunanin al’umma su yarda cewa tsattsauran ra’ayi da ta’addanci suna da dangantaka da Musulunci, alhaki kuwa wannan karya ce da mummunan tunani.
E, akwai kanshin gaskiya cewa, Musulmin da ke da tsattsauran ra’ayi suna fakewa ne da rigar Musulunci. Gaskiya ne cewa ISIS da al-Shabab da Boko Haram duk suna fakewa da Musulunci ne wajen aiwatar da miyagun ayyukansu Domin an taba samun wata kungiya ta makasa da suka yi ta kashe gwamnoni da sarakunan musulmi a daukacin daular musulunci, alhali suna kiran kansu musulmi, suna juya ma’anar dokokin musulunci don kafa hujjar miyagun ayyyukansu.. Ire-iren wadannan sun taba kai wa Makkah hari, inda suka halaka mahajjata, suka jefa gawarwakinsu a rijiyar zam-zam, sannan suka dauke bakin dutse (hajarul aswad) suka tafi da shi gabashin Arebiya har tsawon shekara 25. Kuma wai suna kirtan kansu Musulmi. Akwai Kawarijawa da suka bullo a zamanin halifancin Sayyidina Ali (RA). Wannan dai ba sabon abu ba ne, domin akwai gungun masu tsatttsauran ra’ayi da ke cin zarafin al’umma farar hula. Shin mece ce manufar yakin duniya na daya da na biyu? Wadannan yake-yake biyu sun yi sanadiyyar salwantar da rayuka miliyan 70 zuwa 80. Ko suna da wata dangantaka da Musulunci? Kimanin mutum miliyan 40 suka mutu a yakin duniya na farko; miliyan 60 sun mutu a na biyu. Wannan adadi ne mai yawa. Ga Nagasaki da Hiroshima (a kasar Japan wadanda aka yi wa al’ummarsu ruwan bama-bamai a yakin duniya). Ba da dadewa ba gidan talabijin na CNN ya ruwaito ziyarar Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry a Japan, inda ya halarci taron tunawa da harin bom din Nagasaki da Hiroshima, amma bai nemi afuwar kasarsa ba. Shin wannan ba ta’addanci ba ne; ko kuma me ake nufi da ta’addanci? Wadanda ke da hannu a ta’addanci su ke juya akalar kafafen yada labarai. Sannan an yi wani rahoto a Birtaniya cikin shekarun 1990, wand aka yi wa lakabi da rahoton Rumenede, rahoton dai kan kiyayyar Musulunci ne. Tushen kiyayyar Musulunci (Islamphobia) an bayyana ta da kiyayya mara tushe da tsoron Musulunci da Musulmi. Babu wani dalili na gaskiya. An dai bayyana asalin al’amarin daga abubuwa biyu, wato kafafen yada labarai da ’yan siyasa.

Aminiya: Ko me za ka iya cewa game da maganganun tada hankali da Donal Grumph ke yi wa Musulmi?
Dokta Bilal: Donal Trump yana yi wa kansa barkwanci ne kawai, don daukar hankalin kafafe yada labarai. Yana son juya akalar kafafen yada labarai ne don ya samu goyon bayan jama’ar kasar.
Aminiya: A kasa irin Najeriya, inda mabiya addinan Musulunci da Kiristanci ke zaune tare, ana samun matsala dangane da hanyar da za a bi wajen kawo karshen ta’addanci. Shin ina mafita?
Dokta Bilal: To, ganin yadda ake danganta Musulunci da ta’addanci, wannan ita ce babbar matsalar, don haka ya zama dole a lalubo mafita. Ya kamata a gano ko an taba samun wasu kiristoci a Najeriya da suka aikata ta’addanci? Saboda haka addini kada ya zama ma’aunin aikata ta’addanci. Idan akwai kiristoci masu yaki da ta’addanci, to Najeriya ta yi tafiya da su wajen shawo kan wannan babbar matsalar. Kuma idan akwai kungiyar Musulmi da ke yaki da ta’addanci, ya halatta Najeriya ta yi wannan taro.

Aminiya: Mece ce manufar Musulunci game da daidaito a tsakanin jinsi?
Dokta Bilal: Ina ganin a bai wa mata irin damar da ake bai wa maza. Domin Musulunci ba ya nuna wa maza ko mata bambanci. Sai dai akwai bukatar a bai wa tsarin gina iyuali muhimmanci. A kyautata rayuwar mata ta yadda za su iya daukar dawainiyar kula da ’ya’yansu, musamman kananan yara. Duk da haka idan mace ta zabi yin aiki a wajen gidanta (na aure), a wurin da babu cutarwa ga al’umma, akwai bukatar ta nemi izinin mijinta. Wannan iyali ne na Musulmi. Wasu na iya cewa ai namiji na tafiya aiki a kashin kansa, me ya sa mace za ta nemi izinin mijinta? Wannan ba magana ba ce ta daidaiton jinsi. An dora wa miji nauyin kua da matarsa, inda zai rika samo mata abubuwan da take bukata a gida. Don haka yana da hakkin dora mata alhakin kula da yara da gida. Idan har ta yanke wa kanta matsaya wajen yin aiki a fannin da zai taimaki al’umma da iyalinta, sai ta nemi amincewar mijinta.
Aminiya: Wasu da ke adawa da tsarin rabon gadon Musulunci ba sa ganin adalcin mace ta samu rabin abin da namiji zai samu. Ko za ka bayyana mana hikimar da ke tattare da yin haka?
Dokta Bilal: Idan aka yi magana kan dokar gado a shari’ar Musulunci, namiji na samun rubi biyu na abin da mace za ta samu. Idan ka raba gado, ka bai wa mace kasonta, ka bai wa naminji kasonsa, to namijin an dora masa alhakin kula da macen. Namiji na samu nunki biyun abin da mace za ta samu ne tun da an dora masa alhakin kula da ita. A cikin al’ummarmu ta musulmi wannan shi ne adalci. Sai dai kuma idan ka yi la’akari da al’ummar Amurka su raba daidai suke yi, wannan shi ne irin adalcinsu, tunda namiji da mace kowa cin gashin kansa yake yi; mace na neman abin da za ta kula da kanta, shi ma namiji yana neman abin da zai kula da kansa. Mu dai a cikin al’ummarmu an yi la’akari da dimbin nauyin kula da mace da aka dora wa namiji.

Aminiya: a kasa irin Najeriya, inda addinai biyu na Musulunci da Kirista ke zaune za a iya dabbaka tsare-tsaren Musulunci?
Dokta Bilal: Mafi yawan ’yan Najeriya Musulmi ne. Idan kuwa mafi yawan ’yan Najeriya Kiristoci ne, to Musulmi ba su da hurumi tursasa yin amfani da tsarin tattalin arzikinsu ko na siyasa a kan mafi yawan al’umma. Musulmi sun yi mulki kasar Andalus (Spain) da India na tsawon shekaru, inda suka bayar da kariya ga rayuwar al’umma, suka kuma zauna da su cikin lumana.. Idan kuwa mutane suka fake da addini don neman kuri’u, alhali su ba masu adalci ba ne, sai a dauka suna ci ne da addini. Abin da kawai ya kaamata mutane su lura da  shi, shi ne dabi’ar daidaikun mutane; shin wannan mutumin zai zama adalin jagora, Musulmi ne ko Kirista? Domin abin da ke tafiyar da al’umma shi ne adalci ba fakewa da wani gungun mabiya addini ba.

Aminiya: Wadanne matakai kake dauka don ganin cewa dalibanka ba su ginu a kan tunani irin na masu tsattsauran ra’ayin addini ba?
Dokta Bilal: Abu na farko da ya kamata a fahimta game da Jami’ar Musulunci ta Intanet, shi ne mafi yawan kwasa-kwasanta ba su takaita a kan musulunci kawai ba. Lokacin da na taba ganawa da jaridar Daily Trust karo na farko, ba a fara karatu a sauran sassan ilimi na makarantar ba. Yanzu kuwa, mun fara da kwas din Bankin Musulunci da hada-hadar kudi da ilimin nazarin tunani da harkokin sadarwar zamani, darussa ne da aka bunkasa su a jami’ar. Ba dukansu ba ne suka takaita ga koyarwar Musulunci ba. Sai dai sanin dokokin shari’a da daukacin fannonin da ake koyarwa sun ta’allaka ne ga mahangar Musulunci. Wannan shi ne abin da ya sanya jami’ar ta zama daban, inda mutane masu kwarewa a fannonin Musulunci ke koyarwa. Kuma suaran fannonin ilimi ana koyar da su ne bisa tsarin fafutikar kulla alaka tsakanin fannonin ilimi da Musulunci, ta yadda mutane za su samu horo kan akidar Musulunci managarciya, wadda za ta kange su daga aukawa tarkon tsattsauran ra’ayi. Don haka ake koyar da hakikanin Musulunci, inda ake nuni da muhimmin al’amari a zama tsaka-tsaki. Musulunci dai ya yi mana nuni da mu dauki matsakaiciyar hanya.

Aminiya: Mafi yawan Musulmi ba su san yadda Musulunci ke bai wa harkokin kasuwanci kariya ta hanyar takaful ba. Ko kana ganin takaful za ta a magance matsalar gobara a kasuwannimu?
 Rashin sanin wani abu game da tsarin inshorar Musulunci, wato abin da ake kira Takaful da tsarin bankin Musulunci, duk nakasu ne na masu ilimi a cikin al’umma da suka kasa kafa cibiyar hada-hadar kudi ta hadin gwiwa, da za ta tabbatar da bayar da kariya ga sana’o’i daban-daban. An dai fara yin wannan tsari (na takaful) a zamanin Halifancin Umar bn Khattab, inda ya zabi masu sana’o’i, ya ba su umarnin tara wasu kudi a wani asusu, da manufar tallafa musu idan musifa ta auka wa kasuwancinsu ko sana’arsu. daukacin masu sayar da takalma da suaran masu sana’o’i sun shiga cikin wannan tsarin na zuba kudi a wannan asusu. An kuma adana kudin don taimaka wa masu sayar da takalma da masu yi da masu gyarawa, ta yadda idan wani abu ya samu kasuwancinsu, za a dauko kudin nan a tallafa musu su sake ci gaba da harkokin kasuwancinsu. Wannan shi ne asalin takaful, tun daga tunanin da Halifa Umar dan Khattabi ya yi.