’Yan ta’addan ISWAP sun sace direbobi 4 a Borno
’Yan ta’addan kungiyar ISWAP sun sace wasu direbobin manyan motoci hudu
’Yan ta’addan kungiyar ISWAP sun sace wasu direbobin manyan motoci hudu a Jihar Borno.
Rahotanni na nuna cewar an yi garkuwa da direbobin ne a kusa da kauyen Ngwom da ke Karamar Hukumar Mafa. mai nisan kilomita 50 daga Maiduguri, babban birnin Jihar.
Kazalika, rahotanni sun ce direbobin sun kai leburori wadanda akasarinsu masu sarar itace da lodi zuwa daji lokacin da ’yan ta’adda dauke da makamai suka tare su.
’Yan ta’addan sun tunkari direbobin ne da sunan cewa suna bukatar su yi musu aiki domin kai mambobinsu wani kauye da ke kusa.
Sai dai ba da jimawa ba ’yan ta’addan suka yi garkuwa da direbobin da fasinjojinsu.
“Lokacin da muka yi kokarin rokon a mana afuwa sai, daya daga cikinsu ya ce a tafi da mu kawai nan take,” in ji daya daga cikin ma’aikatan, mai suna Abba.
“Mun yi sa’a saboda sun sake nazarin manufofinsu na kai hari kan leburorin shi ne suka canza shawarar yin garkuwa da mu maimakon far wa leburorin.”
Sai dai direbobin ba su dawo ba,inda daga bisani ’yan bindigar suka shaida wa leburorin cewa an yi garkuwa da direbobin hudu kuma ba za a sake su ba har sai kowannen su ya biya Naira N250,000 a matsayin kudin fansa.
Majiyar ta ce direbobin da aka sace su ne Rawana, Isa, Ba’ana da Bashir.
Harin na baya-bayan nan dai ya nuna yadda kungiyoyin ’yan ta’adda ke ci gaba da garkuwa da mutane a yankin, lamarin da ya zama abin damuwa ga ’yan kasar baki daya.
Kwanan nan kungiyar ta ISWAP ta koma yin garkuwa da marasa galihu, galibi ’yan gudun hijira don neman kudin fansa.
Harkar yin garkuwa da mutane don neman kudaden fansa na samar da makuden kudaden shiga ga ’yan ta’addan.