’Yan takara sun bijire wa taron da Shugaba Macky Sall ya kira
Ana taron ne domin magance rikicin siyasa da kasar ke fama da shi a Diamniadio da ke kusa da Dakar.
’Yan takarar shugabancin kasa 16 da ’yan kungiyoyin farar hula da dama, sun ki halartar zaman da za a shafe kwanaki biyu ana yi a Senegal.
’Yan takarar da ke cikin gungun ‘Aar Sunu’ sun bayyana tattaunawar da Shugaba Macky Sall din ya shirya, a matsayin shirme.
- Akwai yiwuwar tsagaita wutar yaƙin Isra’ila a Gaza albarkacin watan Ramadana
- Abin da ke janyo rigima da gwamnoni — Sanata Siyako
Alimou Barro wanda ya taimaka wajen kafa jam’iyyar Pastef da aka rusa da kuma ke goyon bayan dan takara Bassirou Diomaye Faye da har yanzu yake tsare a gidan yari, na da ra’ayin cewa sanar da jadawalin zaben shugaban kasa ya fi gudanar da zaman tattaunawa.
An fara taron ne domin tattaunawa kan siyasa da Shugaba Macky Sall ya shirya, domin magance rikicin siyasa da kasar ke fama da shi a Diamniadio da ke kusa da Dakar, babban birnin kasar.
Sai dai taron tattaunawar na da matuƙar muhimmanci a yanayin da ake ciki na rikice-rikicen siyasa da na hukumomin da suka ɗage zaben kasar, a cewar Mamadou Ndoye da ke zaman mamba na gungun kawancen jamhuriya APR kuma babban sakataren ‘Ngor Debout a diaspora.
Wasu magoya bayan haɗin gwiwar Benno Bokk Yakaar da ke mulki na goyon bayan gudanar da taron tattaunawar, amma ba su amince da waɗanda kotun tsarin mulki ba ta amince da takararsu ba su shiga taron.
Sai dai a daidai lokacin da aka ƙaddamar da tattaunawar samar da maslahar siyasa a Senegal din, ana samun masu lashe amansu bayan nuna adawa ga taron.
A wata hira da aka yi da dan takara Aly Ngouille Ndiaye mamba na gungun ’yan takarar shugaban kasa a wata kafar yada labarai a Dakar, ya tabbatar da cewa zai halarta.
A wannan yanayi ne a karshen mako a birnin Dakar, wasu kungiyoyi biyu masu fafutuka suka gudanar da wani taron jerin gwano.
DW ya ruwaito cewa, waɗanda suka gudanar da taron akwai na masu adawa kan ɗage zaɓen shugaban kasa, sai kuma ɗayan na masu kawance da gwamnati a kan taron tattaunawar siyasar na kasa wadda za a sanya sabuwar ranar gudanar da shi.