’Yan takaran APC da PDP sun yi yarjejeniyar zaman lafiya a Legas
dan takarar gwamna na jam’iyyar APC na jihar Legas, Mista Akinwumi Ambode da abokin hamayyarsa na jam’iyyar PDP, Mista Jimi Agbaje sun yi alkawarin amincewa da sakamakon zaben gwamna, tare da bin hakkinsu ta hanyar doka idan ba su amince da sakamakon zaben ba.’Yan takarar sun yi alkawarin ne yayin da suka sanya hannu a […]
dan takarar gwamna na jam’iyyar APC na jihar Legas, Mista Akinwumi Ambode da abokin hamayyarsa na jam’iyyar PDP, Mista Jimi Agbaje sun yi alkawarin amincewa da sakamakon zaben gwamna, tare da bin hakkinsu ta hanyar doka idan ba su amince da sakamakon zaben ba.
’Yan takarar sun yi alkawarin ne yayin da suka sanya hannu a yarjejeniyar zaman lafiya a wani zama da ofishin jakadancin kasar Amurka ya shirya a ofishinsa da ke Jihar Legas a wannan makon.
Mista Akinwumi Ambode ya bukaci magoya bayansa su yi hakuri duk da zaben da aka daga don a cewarsa ‘Duk da dage zaben da aka yi mun san cewa ba za a iya dage makomar ’yan Najeriya ba. Saboda haka ina so in yi amfani da wannan dama wajen yin kira ga mutanen Legas su ci gaba da yin hakuri a wannan lokaci. A madadina da magoya bayana ina mai alkawarin kasancewa mai tabbatar da zaman lafiya a lokacin zaben shekarar 2015 da ma bayan zaben. Na yi alkawarin zan amince da sakamakon zaben jihar Legas.’
Shi ma Mista Jimi Agbaje na jam’iyyar PDP cewa ya yi ‘Mun yi alkawari cewa kafin zabe da ranar zabe da kuma bayan zabe ba za mu yi abin da zai kawo tashin hankali a jihar Legas ba. Ya zama dole a kanmu mu shaida wa magoya bayanmu cewa hanyar ci gaba a Legas ita ce mu tabbatar an yi zabe lami lafiya. Saboda haka na yi alkawarin zan bi hakkina ta hanyar doka da oda’.
Jakadan Amurka a Najeriya, James Entwistle ya bayyana cewa Amurka na son ganin an gudanar da zabe lami lafiya a Najeriya.
James Entwistle ya bukaci ’yan takarar da jam’iyyunsu su bi ka’idojin yarjejeniyar zaman lafiyar da suka yi.
‘Wadanda kasar Amurka take goyon baya a wannan zabe su ne mutanen Najeriya, shi ya sa muke son ganin an gudanar da zabe lami lafiya ba tare da wani tashin hankali ba’. Inji shi.