’Yan takarar Gwamnan Yobe a Jam’iyyar APC sun fuskanci cikas wajen mayar da fom

’Yan takarar Gwamnan Jihar Yobe a karkashin Jam’iyyar APC sun hadu da cikas,cikin makonni biyu da shugabannin jam’iyyar suka kulle ofisoshinsu, yayin da masu son tsayawa takarar suka hada da Alhaji Muhammad Yunusa da Injiniya Mustapha Yunusa Maihajja suka zo don mika fom dinsu na takara, sai suka sha da gudu. Saboda hukumar ’yan sanda […]

’Yan takarar Gwamnan Yobe a Jam’iyyar APC sun fuskanci cikas wajen mayar da fom
’Yan takarar Gwamnan Yobe a Jam’iyyar APC sun fuskanci cikas wajen mayar da fom

’Yan takarar Gwamnan Jihar Yobe a karkashin Jam’iyyar APC sun hadu da cikas,cikin makonni biyu da shugabannin jam’iyyar suka kulle ofisoshinsu, yayin da masu son tsayawa takarar suka hada da Alhaji Muhammad Yunusa da Injiniya Mustapha Yunusa Maihajja suka zo don mika fom dinsu na takara, sai suka sha da gudu. Saboda hukumar ’yan sanda ta taka musu burki, inda ta hana su shiga garin Damaturu, fadar gwamnatin jihar, saboda matakan tsaro, kamar yaddadaya daga cikin ’yan takarar ya ce sun fada masa.
Injiniya Maihajja ya bayyana hakan ne ga Aminiya ya yin da ya shigo kofar garin Damaturu, tare da dandazon jama’a magoya bayansa da kuma jami’an ‘yan sanda ma su yawan gaske da suka ja daga  yadda ya ce wannan mataki da hukumar ‘yan sanda ta dauka a ganinsa akwai lauje cikin nadi kuma alama ce mai nuna kan cewar ana so ne a biya wa wasu bukatunsu ne a gwamnatance.
 Don haka a cewarsa abin da aka musu shi da magoya bayansa na hana su shiga garin na Damaturu da nufin mika fom dinsa kamar yadda uwar jam’iyya ta umarta ba komai bane illa kokarin tauye musu hakkinsu na wadanda ke da ikon tsaya wa a matsayinsa na cikakken dan jihar Yobe.
Ya ce, shi ya san cewa, jam’iyyarsu ta APC,  jam’iyya ce da take bin ka’ida da doka a tsakanin mambobinta, wadda hakan ne ma ya sa ya bi dokar da zuwa gari da gari har garin na Damaturu don mika wannan fom na sa da ya cika, amma kuma aka hana shi shiga garin don biyawa wasu bukatunsu, don haka ya ke fatan jam’iyyarsu ta APC  a matakin kasa za ta duba wannan matsala ta sa da idon basira don karbar fom din da zarar ya kai musu a can sakatariya ta kasa da ke Abuja.
Da Aminiya ke tambayar dan takarar akan ko zai dauki wani matakin neman hakkinsa kan abin da aka masa? sai ya amsa da cewar, ai ya yi wuri don bada amsar hakan illa dais hi ya san cewar uwar jam’iyya za ta bi masa kadi kamar yadda ya fadda a baya, domin a cewar sa ita ce ta ce ya zo fadar jihar don mika fom din, don haka ya mika komai ga hannun uwar jam’iyya ta kasa.
 Daga nan sai ya bada hakuri ga magoya bayan sa kan wannan karan tsaye da aka yi masa, tare da nuna musu cewar, hakan ba zai razana shi ba balle ya maida wukarsa cikin kube, maimakon haka ma a halin da ake ciki an kara masa karfin gwiwa ne.