‘Yan takarar Gwamnan Zamfara na APC sun juya wa Gwamna Yari baya
Sakamakon rudanin da aka samu na fitar da dan takarar Gwamna daga jam’iyyar APC a Jihar Zamfara na rashin amincewar da sauran ‘yan takarar gwamnan takwas suka yi akan dan takarar da gwamna mai barin gado Abdulaziz Yari ya yi. An dai bayyana rahoton cewa duk ‘yan takarar Gwamnan sun haxu gana a Abuja inda […]
Sakamakon rudanin da aka samu na fitar da dan takarar Gwamna daga jam’iyyar APC a Jihar Zamfara na rashin amincewar da sauran ‘yan takarar gwamnan takwas suka yi akan dan takarar da gwamna mai barin gado Abdulaziz Yari ya yi.
An dai bayyana rahoton cewa duk ‘yan takarar Gwamnan sun haxu gana a Abuja inda suka tattauna akan dan takarar da Gwamnan ya tsayar a matasyin wanda zai gaje shi na jam’iyyar APC.
Tun a ranar 9 ga Satumba Gwamna Yari ya tsaida kwamishinan kudin jihar Mukhtar Idris a matsayin dan takarar Gwamna a zaben shekara mai zuwa. Hakan ya sa sauran ‘yan takarar Gwamnan takwasb suka hada kai don kalubalantar dan takarar da Gwamnan ya tsayar.
‘Yan takarar Gwamnan jihar sun hada da: Mataimakin Gwamna Yari tun daga shekarar 201, Ibrahim Wakala da Sanata Kabiru Garba Marafa, da tsohon Gwamnan jihar, Mahmuda Aliyu Shinkafi, da Ministan tsaro Mansur Dan-Ali, da Dauda Lawal, da dan majalisar wakilai Aminu Jaji, da Abubakar Magaji da kuma Sagir Hamidu.