’Yan tankasu

A rana ta babban lauje ga watan Farin-biri na shekara ta dubu karamin lauje da sili da tsayuwa bisa kafa daya, na ga yadda ’yan tankasu suka addabi matasan Haurobiya. Wadannan ’yan tankasu,” sanannu ne a ajujuwan farfajiyar makarantar Dodorido da ke Amintattar jaridar kasar Haurobiya, musamman in an yi la’akari da cewa mun taba […]

’Yan tankasu
’Yan tankasu

A rana ta babban lauje ga watan Farin-biri na shekara ta dubu karamin lauje da sili da tsayuwa bisa kafa daya, na ga yadda ’yan tankasu suka addabi matasan Haurobiya. Wadannan ’yan tankasu,” sanannu ne a ajujuwan farfajiyar makarantar Dodorido da ke Amintattar jaridar kasar Haurobiya, musamman in an yi la’akari da cewa mun taba yi musu lakabi da ’Yan tasku masu faso. To a makon da ya arce na fasko yadda ’yan tasku masu faso suka zama ’yan tankasu masu fashin kayan sana’a, domin su ba su da sana’a.
’Yan tankasu
Masu yankan fankasu
Taron su susu    
An maisheku ’ya’yan kusu
An yi muku hudubar iblisu
Kun kusa fara musu
Ku daina mutsu-mutsu
Da ku jaki zai yi tutsu
’Yan tasku masu faso\
A kiyayi wasoso
Ku yi wanka da sabulu da soso
Ku taka rawar koroso
Kashedinku jaba da kusu!
daukacin matasan da ke laluben na-koko wajen tallata hajarsu a titunan Harubja, Babban birnin Haurobiya, ba zai dade yana jan zarensa ba, matukar bai iya allan-baku da masu fashin kayan sana’a ba. Batu na ingarman karfe, mafi yawan ’yan tankasu ’yan iskan gari ne aka dauka aiki a Hukumar Kula da Muhalli, alhali suna da ‘dan hali’ Domin mu da muke kiransu ’yan tasku masu faso, a lokacin da suke farfasowa, su farfasa wa mutane kayan sana’a, ko ma su yi musu samartakar kusu, ashe har dan tsoho kyamus-kyamus ma ba su kyale shi ba. A dunkule dai ina mai sanar da ku a bakin wani dan tsoho da na ji  ya yi bayanin babbar matsalarsa a sana’a, da wakilin akwatimn magana na kasar Jamus ya gana da shi.
“Ni dai matsala a sana’a ’yan tankasu, musamman ganin yadda suke matsa mana. Sukan kwashe mana kayan sana’a,” inji shi.
Da fatan dai ’yan makaranta kun hau motar zuwa gano. ’Yan tankasu dai firda-firdan karti ne, da hukumar kula da muhalli ta birnin Harubja ta dora musu alhakin kama masu yawon tallace-tallace. Maimakon kula da muhalli, sai dan hali kawai suke yi. Idan kuwa haka ne, to ko so ake yi matasa su daina neman na kansu, su yi ta kashe fatari da gararamba a cikin gari?
Zaluncin ‘’yan tankasu ya fito karara a zamanin mulkin mulka’u na Jam’iyya mai dan boto da sanda jirge. Uwa-uba, kauran Baubawan-cici, wadda shi ne Magajin garin Haurubja, babu abin da yake tsinanawa wajen Karen matasa daga ’yan tankasu, don an ce shi ne ya daure musu kugu, ya umarce su yi ta ruwan balbalin bala’i a kan al’umma. Ganin irin ta’addancin da ’yan tankasu ke tsuwurwurtawa, ma iya yanke hukunci cewa ‘da Bala da bala’i, ba su da bambanci.’
Da yake na ziyarci birnin Tagadas a shekarar da ta arce, na kuma yi arba da masu sana’a a kasuwanni da masu tallata haja a tituna da lungu-lungu, ina kuma da tabbacin cewa ba a tsangwame su ba. Duk da cewa kasar Niyyar-jari na fama da sasarin talalar talauci, amma masu sana’a sun samu sa’ar watayawa. Don haka amtasansu a ko’ina suke ba malalata ba ne; da sun samu damar sana’a sai su yi, tunda Malam Mai yaren Hauhau wajen hawansa ba tare da sa-in-sa ba, ya ce, “Sana’a sa’a, rashin sana’a sata.” Wai gidan lagwada  ya yi nisa, tsunsun kolo ya hango masai.
Abin da nike son nusar da mahukunta a birnin Haurubja, shi ne, mafi yawan wadannan ’yan tankasu ’yan isakan gari ne, kamar yadda mutane ke ganinsu, amma ni ina ganinsu a ’yan sheke aya ne; wato ba ‘’yan iska ba ne, ‘Jakadun sheke aya.’ Don haka ma da zararr sun wawuri kayan masu sana’a, sai ka gansu a wurin ‘’yar raha, suna ta rahi ma raha,’ wato dai an samu ’yar raha a arha, sai a yi ta raha a bariki. Lallai matasa a taka musu burki; hukumomi ku ja musu linzami, domin akwai yiwuwar a yi “Juyin wainar matar manomi.’
Ku kuwa matasa masu fuka-fukan tashi, kada ku bari a yi muku karkaf; ku jajirce wajen sana’a, don kada a yi muku wakaci ka tashi. Babbar mafita dai ku yi kokarin cin jarabawar rayuwa, wato a duk lokacin da kuke neman sa’ar sana’a, sai ku yi karatun wasikar jakin-dawa da na-gida, don fasko alfanun da ke tattare kwazonku, tare da yadda za ku taka ku kai mataki na sama. A rika kokarin samun rumfar kasuwa, domin rage zaluincin azzalumai, inda daidaiku suka gaza, to sai a tafi a kungiyance. Sannan a kiyayi sheke ayar bariki; kuma ku nemi sanin dabarun sarrafa dukiya bisa tsarin zdamani ta yadda ba za a layance muku a kowane bagiren rayuwa ba.
’Yan tankasu ko ’yan tasku masu faso, ko dai kun zama ’yan tasku masu fashi? Ku gyara halinku, ku daina dan hali; ku nemi hukumar irnin Haurubja ta yi muku tsari mai kyau. Domin na jiwo cewa kwananan za ta kara zabgeku, watakila kuma abin da kuka ji ke nan, shi yasa in kun kama mai laluben na-koko a kan titi sai kawai ku karbi rabonku, ku kyale shi. Wai ’yan tankasu tunda kuna da karfin ingarman doki, me zai hana ku koma kauyukanku ku fadi kasa ku yi ta sana’ar na-duke, maimakon ku bari hukuma na amfani da ku ta hanyar da ba ta dace ba? Duk irin fashin da za ku yi wa talakawa, ku hana su sana’a, ba za ku yi kwashi kwaraf da wadakar da mahukunta ke yi a Haurobiya ba. ‘Idan na-zomo ya ji, to gangar jiki ta tsira,’ daga abin da zai je, ya komo. To kun ji, ehe!

Sabon mai shela
Makarantarmu a wannan makon ta kaddamar da sabon mai shela, wanda ya taso daga birnin Tagadas. Mai shela ka dauki bututun batutuwan makaranta, don tabbatar wa Haurobiyawa yadda za inganta zamantakewa ba zaman-takewa ba; tattalin-dukiya, ba talalar talauci ba; tsayayyar siyasa ba wasan Samson Siya-siya da kwakwalen al’umma ba.