’Yan tawaye sun kai hari makarantar horas da jami’an tsaro a Mali

Masu zuwa Sallar Asuba sun ce karar harbe-harben ta sa sun koma gidajensu

’Yan tawaye sun kai hari makarantar horas da jami’an tsaro a Mali

Sojojin kasar Mali (Photo by ANNIE RISEMBERG / AFP)

’Yan tawaye sun kai hari a makarantar horas da jami’an tsaron Jandarma da ke yankin Faladie a Bamako, babban birnin kasar Mali.

Da asubahin ranar Talata ne mazauna sassan birnin Bamako suka ce sun ji karar harbin bindigogi masu razanarwa sosai.

Wadanda suka je masallacin don halartar Sallar Asuba sun ce karar harbe-harben da aka fara da misalin karfe 5.30 na asuba agogon GMT, ta sa su komawa gidajensu.

Rundunar sojin Mali ta tabbatar da harin na Faladie, amma ta sanar da cewa birnin Bamako na karkashin ikonta.

Sanarwar ta ce, “Da safiyar yau ne gungun wasu gungun ’yan ta’adda suka yi yunkurin kutsawa cikin makarantar horas da Jandarma da ke Faladie.

“A halin yanzu ana ci gaba da gudanar da aikin sharar mutane a duk fadin yankin,” in ji sanarwar.

Rundunar ta yi kira ga mazauna yankin da su kauce wa yankin, su jira sanarwa a hukumance.

Wasu mazauna sun ce karar harbin na fitowa ne daga bangaren filin jirgi, wasu kuma sun ce daga bangaren jami’an tsaro ne.

Faladie yanki ne da ke Kudu maso Gabashin Bamako kusa da babban filin jirgin sama na kasa da kasa.

Mali daya ce daga cikin kasashen yammacin Afirka da ’yan tawaye masu ikirarin jihadi suka adabba tun daga shekara ta 2012, a arewacin kasar.

Daga nan ne mayakan suka bazu a yankin Sahel da kuma a baya-bayan nan zuwa Arewacin kasashen da ke gabar teku.

An kashe dubban mutane tare da raba miliyoyi da gidajensu a yankin a yayin da sojojin kasar suke kokarin yakar ’yan ta’addan, duk da cewa ana zargi kowane bangare da cin zarafin fararen hula.

Rashin gamsuwa da salon yaki da mayakan ya sa taimaka wajen kifar da gwamnati sau biyu a Mali. Haka ma an samu juyin mulki a makwabciyarta Burkina Faso da kuma Nijar.

Sai dai hare-haren ’yan jihadin sun kara ta’azzara duk da alkawurran da gwamnatin sojin kasar ta yi na inganta tsaro, ciki har da maye gurbin kawancensu da kasashen yammacin Turai da kulla kawance da Rasha.

Cikin alkawurin har da da amfani da sojojin haya daga sojojin Wagner na Rasha masu zaman kansu wajen kawar da maharan.

Amma an kashe wasu gogaggun mayakan Wagner a karshen watan Yuli a lokacin wani fafatawa tsakanin ’yan tawayen Abzinawa da sojojin Mali, wadanda mayakan suka yi musu kwanton bauna.

NAFDAC ta gano wani jabun maganin malaria da ke yawo a Najeriya

Kotu za ta karɓi shaidar wakilin Aminiya a shari’ar garkuwa da mutane

An daƙile harin ’yan ta’adda a Borno

An bai wa tsofaffin ’yan bindiga 6 shaidar tuba a Yobe