’Yan tawaye sun kashe gomman sojoji a Mali

Rundunar sojin Mali ta ce faɗan da aka yi a Anefis ranar 12 ga Yuli ya yi sanadin mutuwar sojoji 30 tare da jikkatar kusan 60.

’Yan tawaye sun kashe gomman sojoji a Mali

Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa ’yan tawaye na ƙabilar Abzinawa sun kashe gomman sojojin Mali bayan da aka yi wa ayarinsu kwanton-ɓauna a safiyar Asabar a garin Anefis da ke arewacin ƙasar.

Wata majiya daga Gao ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa an kai wa ayarin farmaki ne a kan hanyar Anefis zuwa Gao, kusa da Tabankort, inda aka ce an yi gumurzu mai tsanani.

Ita ma ƙungiyar Front de Libération de l’Azawad (FLA), wadda aka kafa a watan Nuwamba 2024, ƙungiyar ’yan tawayen Touareg da ke fafutukar neman ’yancin kai da kuma ’yantar da yankin Azawad (wanda ya ƙunshi yankunan Gao, Tombouctou, Kidal, Menaka, da Taoudenit) a arewacin Mali, ta tabbatar da kai harin.

Wani jami’in tsaro da ya nemi a sakaya sunansa ya ce harin ya yi wa sojojin Mali mummunar ɓarna, duk da cewa wasu daga cikin ayarin sun samu nasarar ci gaba da tafiya.

A wasu hotuna da FLA ta wallafa, ƙungiyar ta yi iƙirarin kama gomman sojojin Mali a yayin harin.

A ranar 4 ga watan Yuli ne haɗaɗɗiyar ƙungiyar ’yan tawaye ta ƙabilar Abzinawa da mayaƙan JNIM suka ƙwace garin Anefis na ɗan lokaci a wani jerin hare-hare da suka kai a arewacin Mali.

Tun da farko, rundunar sojin Mali ta ce faɗan da aka yi a Anefis ranar 12 ga watan Yuli ya yi sanadin mutuwar kusan sojoji 30 tare da jikkatar kusan 60.

Sai dai kwanaki biyu kafin hakan, sojojin Mali tare da mayaƙan haya na Rasha sun sanar da sake ƙwato garin bayan kwanaki ana gwabza faɗa da ’yan tawayen.