’Yan tawaye sun kashe wa Nijar sojoji 7, wasu 5 sun mutu a hatsarin mota

An kashe 7, wasu biyar kuma sun mutu a hatsarin mota suna kokarin mayar da martani

’Yan tawaye sun kashe wa Nijar sojoji 7, wasu 5 sun mutu a hatsarin mota

Wasu sojoji suna sintiri a Kudancin Jamhuriyar Nijar. (Hoto: Giles Clarke)

Wasu da ake zargin ’yan tawaye ne sun kashe wa Jamhuriyar Nijar sojoji bakwai, wasu biyar kuma sun mutu a hatsarin mota lokacin da suke kokarin kai ɗauki a yankin Tillaberi.

Mace-macen na ranar Alhamis na zuwa ne a daidai lokacin da kasar Faransa, wacce ta yi mata mulkin mallaka ke shirye-shiryen janye dakarunta masu yaki da ta’addanci daga kasar.

Ministan Tsaron Nijar, Salifou Moudy, ya fada a cikin wata sanarwa cewa, “Wasu daruruwan ’yan ta’adda sun kai hari kan sojojinmu a garin Kandaji a ranar Alhamis. An kashe mana sojoji bakwai a sakamakon haka.

“A lokacin da muka yi kokarin mayar da martani, sai dakarunmu suka yi mummunan hatsari, inda biyar daga cikinsu suka rasu,” in ji shi.

Ya kuma ce wasu ƙarin sojojin bakwai sun ji rauni kuma yanzu haka suna can an garzaya da su asibiti.

“Tuni muka fara farautar wadanda ke da hannu a ciki, kuma za su ɗanɗana kuɗarsu,” in ji Ministan.

Yankin Tillaberi dai na kan iyakar kasar mai kusurwa uku da ta haɗa kasashen Nijar da Mali da kuma Burkina Faso.

Wajen dai ya yi kaurin sunan kasancewar maɓoyar ɓata-gari, musamman ’yan tawayen da ke da alaka da kungiyoyin Al-Qaeda da IS.

Tags