’Yan tawaye sun kwace garin Bentiu mai arzikin mai a Sudan ta Kudu
’Yan tawayen Sudan ta Kudu sun sake kwace garin Bentiu mai arzikin man fetur daga dakarun gwamnati kamar yadda kakakinsu ya ce.Birgediya Janar Lul Ruai ya umarci kamfanonin hakar mai su hanzarta dakatar da aikin hakar man kuma su kwashe ma’aikatansu daga garin cikin mako daya.Sai dai kakakin sojan kasar Sudan ta Kudu ya musanta […]
’Yan tawayen Sudan ta Kudu sun sake kwace garin Bentiu mai arzikin man fetur daga dakarun gwamnati kamar yadda kakakinsu ya ce.
Birgediya Janar Lul Ruai ya umarci kamfanonin hakar mai su hanzarta dakatar da aikin hakar man kuma su kwashe ma’aikatansu daga garin cikin mako daya.
Sai dai kakakin sojan kasar Sudan ta Kudu ya musanta cewa garin ya fada hannun ’yan tawayen, inda ya ce har zuwa shekarajiya Laraba ana fafata fada a tsakaninsu. bangarorin biyu sun rika zargin juna da keta yarjejeniyar tsagaita wuta da suka cimma a watan Janairu.
Fiye da mutum miliyan daya ne aka raba da muhallinsu bayan barkewar fada sakamakon zargin da Shugaban Sudan ta Kudu Salba Kiir ya yi ga korarren mataimakinsa Riek Machar na yunkurin juyin mulki.
Machar ya musanta zargin, amma daga baya ya kaddamar da tawaye da niyyar kifar da gwamnatin Mista Kiir.
Sojojinsa sun kwace garin Bentiu hekdwatar Jihar Unity jim kadan da fara fafatawa. Sai dai sojojin gwamnati sun fatattaki ’yan tawayen daga birnin a ranar 10 ga Janairu. Kudin shiga daga arzikin mai a Sudan ta Kudu ya yi kasa da kashi 20 cikin 100 bayan barkewar rikicin.
kasashen China da Rasha ne suka fi zuba jari a harkar mai a kasar, kuma Birgediya Janar Lul Ruai ya gargadi kamfanonin cewa kada su ki bin umarnin rufe harkokinsu. In kuma suka ki “za a rufe su da karfi kuma rayuwar ma’aikatansu na iya shiga hadari,” inji shi.
Wani jami’in Majalisar dinkin Duniya a Sudan ta Kudu mai suna Joe Contreras, ya ce sojojin kiyayen zaman lafiya na kasar Mongoliya sun ceto ma’aikata 10 na kamfanin hakar mai na Rasha mai suna Safinat a kusa da Arewacin Bentiu a ranar Litinin kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AP ya ruwaito.
Ya ce biyu daga cikin ma’aikatan biyar da aka raunata suna cikin mummunan yanayi.
Kakakin sojin Sudan ta Kudu, Kanar Philip Aguer ya ce mummunan fada na ci gaba da gudana don iko da birnin na Bentiu kamar yadda AFP ya ruwaito. “Sojojin ’yan tawaye sun yi kokarin shiga wani bangare na garin amma an mayar da su baya,” ya shaida wa AFP.
Sudan ta Kudu dai ta samu ’yancin kai daga kasar Sudan ne a shekarar 2011 bayan dogon yaki, inda ta zamo kasa ta baya-bayan nan da ta samu ’yancin kai a duniya.