’Yan tawaye sun kwace sansanin soji na 4 a Mali
’Yan tawayen Azbinawa a Mali sun yi ikirarin kwace karin sansani na hudu na sojojin kasar bayan musayar wuta a yankin Gao
’Yan tawayen Azbinawa a Mali sun yi ikirarin kwace sansani na hudu na sojojin kasar bayan musayar wuta a yankin Gao.
Kakakin kungiyar ’yan tawayen da ke neman kafa sasar Azawad, Mohamed Elmououd Ramadane ya ce sun kwace sansanin na Bamba ne bayan artabun na ranar Lahadi a yankin Gao da ke Arewacin kasar.
- Shin ƙungiyar ƙwadago za ta janye yakin aiki?
- NAJERIYA A YAU: ‘Bai kamata ƙarin albashi ya tsaya a wata shida ba’
Sansanin na Bamba shi ne na hudu da mayakan na Azawad suka yi ikirarin kwacewa a tsawon wata biyu da ’yan tawayen na suka kaddamar da hare-hare bayan ficewar dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya daga Mali a watan Agusta.
Kafin shi, mayakan sun yi ikirarin kwace sansanin Bamba sun yi ikirarin sansanoni sojin da ke Lere, da Dioura da kuma Bourem.
Sai dai rundunar sojin kasar ta sanar ta shafinta na X cewa dakarunta na musayar wuta da ’yan tawayen, kuma nan gaba za ta fitar da karin bayani.
Shekaru takwas ke nan da mayakan na Azawad suka ajiye makamansu bayan kulla yarjejeniya da gwamnati.
Sai dai sun dade suna korafin mahukuntan kasar da watsi da yarjejeniyar.
A shekarar 2012 ne suka fara bore kafin daga sojojin Faransa su taimaka wajen fatattakarsu daga manyan biranen da suka kame.