’Yan tawaye sun mika wuya a Libya

’Yan tawayen qasar Libya da ke iqirarin shugabancin qasar a birnin Tripoli sun miqa iko ga gwamnatin da ke samun goyon bayan Majalisar Xinkin Duniya.An bayyana matakin ne a wata sanarwa da aka wallafa a shafin yanar gizon ma’aikatar shari’ar qasar.Sanarwa a madadin gwamnatin ‘yan tawayen mai kiran kan ta gwamnatin ceton qasa ta ce, […]

’Yan tawaye sun mika wuya a Libya
’Yan tawaye sun mika wuya a Libya

’Yan tawayen qasar Libya da ke iqirarin shugabancin qasar a birnin Tripoli sun miqa iko ga gwamnatin da ke samun goyon bayan Majalisar Xinkin Duniya.
An bayyana matakin ne a wata sanarwa da aka wallafa a shafin yanar gizon ma’aikatar shari’ar qasar.
Sanarwa a madadin gwamnatin ‘yan tawayen mai kiran kan ta gwamnatin ceton qasa ta ce, ta sauka ne a bisa buqatun ‘yan qasar da kuma kaucewa zub da jini.
Hakan na zuwa ne mako guda bayan da sabon Firaministan Gwamnatin Haxin kan Qasar Fayez al-Sarraj ya isa birnin Tripoli.
Sabuwar gwamnatin Libyar ta tare a Tripoli babban birnin kasar ne a makon jiya da nufin karve ikon qasar, kuma tun a wannna lokacin tana gudanar da al’amuranta a wani sansanin sojin ruwa.
Har yanzu dai qasar ta Libya na da hukumoni daban-daban da basa ga maciji da juna da ke zaune a gabashin qasar da kuma Tripoli babban birnin qasar.
Gwamnatin wacce qasashen duniya ba su amince da ita ba, ta riqe mulkin ne tun a shekarar 2014, bayan wata arangama tsakanin qungiyoyin masu riqe da makamai a birnin Tripoli, da ya tilsatawa zavavviyar gwamnatin tserewa zuwa gabasghin qasar.
Matakin baya-bayan nan zai bayar da dama ga sabuwar gwamnatin haxin kan da ke da goyon bayan Majalisar Xinkin Duniya rike ragamar ikon qasar da ke fama da rarrabuwar shugabanci.