’Yan tawaye sun yi garkuwa da mutum 39 a Colombia
ELN, wadda ta daɗe tana tayar da ƙayar baya a Colombia, na samun kuɗaɗen shiga ne ta hanyar fataucin miyagun ƙwayoyi.
Ƙungiyar ’yan tawaye ta National Liberation Army (ELN), wadda ita ce mafi girma da ke ci gaba da ɗauke da makamai a Colombia, ta yi garkuwa da mutum 39, ciki har da ƙaramin yaro, a yankin Choco da ke arewa maso yammacin ƙasar.
Sojojin Colombia sun ce an sace mutanen ne a kan wata babbar hanya, yayin da wata majiya ta tsaro ta tabbatar da cewa dukkan waɗanda aka yi garkuwa da su fasinjoji ne da ke tafiya cikin motar bas.
- Gwamnatin Kebbi za ta yi wa mutum 300 auren gata
- Manchester United ta ɗauki Youri Tielemans daga Aston Villa
Rundunar sojin ta buƙaci ƙungiyar ELN ta saki mutanen ba tare da wani sharaɗi ba, tana mai jaddada cewa rayuwarsu na cikin haɗari.
Ƙungiyar ELN, wadda ta daɗe tana tayar da ƙayar baya a Colombia, na samun kuɗaɗen shiga ne ta hanyar fataucin miyagun ƙwayoyi da sauran haramtattun ayyuka, inda take da ƙarfi musamman a yankin Choco da ke iyaka da ƙasar Panama.
Ƙoƙarin gwamnatin Shugaba Gustavo Petro na cimma yarjejeniyar zaman lafiya da ƙungiyar ya ci tura tun bayan hawansa mulki a shekarar 2022.
Shugaban ƙasar da aka zaɓa, Abelardo de la Espriella, ya yi alƙawarin ɗaukar tsauraran matakai kan ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai domin dawo da tsaro a ƙasar.