‘Yan tawayen Houthi sun kai wa Saudiya hari da makami mai linzami karo na biyu
Gamayyar kasashen da Saudiyya ke jagoranta a yakin da ake yi da ‘yan tawayen Houthi na kasar Yemen ta ce ta tare wani makami mai linzami da aka harba birnin Riyadh, kamar yadda kafafen watsa labaran Saudiyya suka sanar. Ganau na yadda lamarin ya auko a babban birnin kasar Saudiyya sun wallafa wani faifan bidiyo […]

Gamayyar kasashen da Saudiyya ke jagoranta a yakin da ake yi da ‘yan tawayen Houthi na kasar Yemen ta ce ta tare wani makami mai linzami da aka harba birnin Riyadh, kamar yadda kafafen watsa labaran Saudiyya suka sanar.
Ganau na yadda lamarin ya auko a babban birnin kasar Saudiyya sun wallafa wani faifan bidiyo a shafukan sada zumunta da ke nuna hayaki ya turnuke sararin samaniya kuma an ba da rahotannin rushewar wurare kamar yadda BBC ta ruwaito.
Gidan talabijin na al-Masirah na ‘yan tawayen Houthi ya bayar da rahoton da ke cewa mayakan kungiyar sun harba makami mai linzami samfurin Burkan-2 kan fadar Yamama
Wani makami mai linzami da ‘yan tawayen suka harba a watan jiya ya kusa fada wa kan filin jirgin saman Riyadh.
Saudiyya da Amurka sun zargi Iran da bai wa ‘yan tawayen Houthi makamai masu linzami, duk da cewa kasar ta Iran ta musanta zargin.
Tun a shekarar 2015 ‘yan tawayen ke yakar gwamnatin Yemen da kuma gamayyar kasashen da Saudiyya ke jagoranta wajen yakin.