’Yan tawayen Siriya sun samu sabon shugaba
kungiyar ’yan tawayen Siriya ta Ahrar al-Sham ta bayyana sabon shugaba bayan mutuwar Hassan Abboud a wani farmaki bam a garin Ram Hamdan da ke lardin Idlib.A shekaranjiya Laraba ne, kungiyar ta bayyana Hashim al-Sheikh wanda ake kira Abu Jaber, a matsayin sabon shugabanta. Sai Abu Saleh Tahan da aka nada a matsayin mataimakinsa. Har […]
kungiyar ’yan tawayen Siriya ta Ahrar al-Sham ta bayyana sabon shugaba bayan mutuwar Hassan Abboud a wani farmaki bam a garin Ram Hamdan da ke lardin Idlib.
A shekaranjiya Laraba ne, kungiyar ta bayyana Hashim al-Sheikh wanda ake kira Abu Jaber, a matsayin sabon shugabanta. Sai Abu Saleh Tahan da aka nada a matsayin mataimakinsa.
Har ila yau, kungiyar ta yi kira da mambobinta da su ci gaba da yakin da suke da gwamnatin Siriya, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito.
kungiyar Kare Hakkin dan Adam da take bin diddigin rikicin wato (Syrian Obserbatory for Human Rights) ta ce tsohon shugaban kungiyar ’yan tawayen ya gamu da ajalinsa ne a daidai lokacin da yake taro da shugabanin kungiyoyin adawar kasar kimanin su 50. Kodayake, har zuwa lokacin hada wannan rahoton babu wani da ya dauki alhakin harin. Amma an zargin kungiyar kasar Musulunci ta IS da kashe wani jagoran kungiyar a farkon shekaran nan. Kuma Mista Hassan din ya taba yin Allah-wadai da kungiyar da kuma bayyana ta cewa “tana bata sunan addinin Musulunci ne kawai” a lokacin wata zantawa da kafar yada labarai ta BBC a watan Yunin da ya wuce.
Taron dai ya gudana ne a lardin Idlib, wanda ya tattaro ’yan kungiyar Ahrar da kuma sauran kungiyoyin adawa da ke cikin yakin basasar kasar, ciki har da kungiyar Abdallah Azzam da kuma Iman brigades, a wani mataki na tattauna yadda za su tunkari yaki da kungiyar kasar Musulunci.