’Yan tawayen Sudan ta Kudu sun kai hari a Malakal
Wani jami’in sojan Sudan ta Kudu ya ce fada ya dawo a kasar bayan da ’yan tawaye suka kai hari ga sojojin kasar a garin Malakal hedkwatar Jihar Upper Nile da ke da albarkatun man fetur duk da yarjejeniyar tsagaita wuta da aka kulla a tsakaninsu.Wani jami’in gwamnati ya tabbatar da cewa ’yan tawayen sun […]
Wani jami’in sojan Sudan ta Kudu ya ce fada ya dawo a kasar bayan da ’yan tawaye suka kai hari ga sojojin kasar a garin Malakal hedkwatar Jihar Upper Nile da ke da albarkatun man fetur duk da yarjejeniyar tsagaita wuta da aka kulla a tsakaninsu.
Wani jami’in gwamnati ya tabbatar da cewa ’yan tawayen sun isa garin kuma sun kwace rabin gari a ranar Talatar da ta gabata. Kuma Majalisar dinkin Duniya ta ce ana fafata mummunar fada a kusa da ginin sojin kiyaye zaman lafiya da ke kusa da filin jirgin saman garin, kuma musayar wutar da ake yi na shafar ginin.
Kakakin sojojin Sudan ta Kudu Philip Aguer ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na AP cewa fada ya barke ne a ranar Talata a garin Malakal wand a baya ke hannun ’yan tawaye amma yanzu sojojin gwamnati ke iko da shi.
“Fadan ya yi zafi, kuma ana fafatawa a wajen garin. Babban hari ne da aka tsara shi sosai,” wani ganau ya shaida wa AP.
Duk da cewa bangarorin da ke fada da juna sun sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a ranar 23 ga Janairu, sai dai sun rika zargin juna da keta yarjejeniyar.
Majalisar dinkin Duniya ta zargi bangarorin biyu da keta hakkin jama’a, kuma a ranar Litinin da ta gabata, sojojin Sudan ta Kudu sun bayar da sanarwar cewa ana tuhumar fiye da sojojin gwamnati 20 kan kashe fararen hula.
Kakakin Odfam a Sudan ta Kudu Grace Cahill ta ce rukunin masu dauke da makamai sun taru a wajen ginin Majalisar dinkin Duniya a Malakal, inda mutum dubu 27 ke zaman mafaka. “Kasancewar masu dauke da makamai a wajen gini yana matukar firgita mazauna cikin ginin,” inji ta.
An kashe dubban mutane tare da raba fiye da mutum dubu 800 da muhallinsu sakamakon barkewar rikicin a tsakiyar Disamban bara, bayan da sojojin da ke gadin Fadar Shugaban kasar da ke Juba, suka fara fada a tsakaninsu, inda fadan ya watsu zuwa sassan kasar.
Korar tsohon Mataimakin Shugaban kasar Mista Riek Machar a bara ne ta jawo rikicin kabilancin da ya raba kan sojojin kasar.
Sojoji ’yan kabilar Nuer ta Mista Machar sun koma bangaren ’yan tawayen da ke karkashinsa, yayin da sojoji ’yan kabilar Dinka ta Shugaba Salba Kiir suke gefensa.