’Yan uwan da suka yanke hulda har tsawon shekara 25 sun sasanta a Arfa

Ani da Marya, ’yan uwan da suka yanke ma’amala da juna har na tsawomn shekara 25, sun hadu a ranar Arfa. Sabanin ’yan uwan ya samo asali ne a sanadiyyar kin amincewar da mahaifiyar Ani ta yi a bata gadon mahaifinta, sun sasanta da juna.Bayan da aka bai wa Ani rabonta na gado, sai ta […]

’Yan uwan da suka yanke hulda har tsawon shekara 25 sun sasanta a Arfa

Ani da Marya, ’yan uwan da suka yanke hulda tsawon shekara 25Ani da Marya, ’yan uwan da suka yanke ma’amala da juna har na tsawomn shekara 25, sun hadu a ranar Arfa. Sabanin ’yan uwan ya samo asali ne a sanadiyyar kin amincewar da mahaifiyar Ani ta yi a bata gadon mahaifinta, sun sasanta da juna.
Bayan da aka bai wa Ani rabonta na gado, sai ta kaurace wa ’yan uwanta. Ita da mijinta suka bar kauyensu, inda iyayenta ke da zama. Amma a wannan haduwar tasu, sai suka rungume juna, suna ta kukan dadi, tare da nuna takaicin al’amarin da ya faru, har ta kai ga rabuwarsu.
Jaridar Okaz ta kasar Saudiyya, ta ruwaito cewa, Ani ta sha yin yunkurin zuwa ta dubo ’yan uwanta, don jin halin da suke ciki, amma mijinta sai ya tursasata kan lallai ta zaba, ko dai ta ci gaba zama tare da ’ya’yanta, ko kuma ya saketa, matukar tana son yin hulda da ’yan uwanta.
Bayan rabuwarta da ’yan uwa, sai Ani ta nemi aiki a kasashen Larabawa da kuma kasashen yankin Tekun Fasha, saboda halin rayuwa da ta samu kanta da ’ya’yanta a ciki. Wannan dalili ya sanya ta fara aiki a wajen gidan mijinta, har ta hadu da wasu iyalai a yankin Tekun Fasha, wadanda suka tafi da ita zuwa aikin hajjin bana.
Ta kuma kuduri aniyarta ziyartar ’yan uwanta da zarar ta koma kasar Indonesiya. Ta kuma jadadda cewa ba za ta sake rabuwa da su ba, musamman bayan da ta smau labarin cewa, bayan tafiyarta mijinta ya samu wata matar.

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu

Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan