‘Yan wasan Firimiyar Najeriya da suka koma taka leda a kasar waje

Jerin ’yan wasan Gasar Firimiyar Najeriya da suka koma taka leda a kasashen waje.

‘Yan wasan Firimiyar Najeriya da suka koma taka leda a kasar waje

Gasar Firimiyar Najeriya ta kara samun tagomashi matuka a shekarun da suka gabata, musamman ganin yadda zaratan ’yan wasa kwararru suke taka leda a gasar har daga kasashen waje ciki har da Brazil.

Aminiya ta ruwaito yadda gasar ta yi zafi a kakar bara, inda har sai a wasan karshe ne aka iya sanin kungiyar da ta lashe gasar.

  1. Wane tasiri dawowar Cristiano Ronaldo zai yi wa Man-U?
  2. An kama masu kai wa ’yan bindiga mai a Katsina

Kungiyar Akwa United ce ta lashe gasar da maki 71, wanda shi ne karo na farko da kungiyar ta lashe gasar a shekara 25 da kafa ta.

Burin duk dan wasan da ke taka leda a Najeriya bai wuce ya samu damar ficewa zuwa kasar waje ba, inda ake ganin ya fi nan ci gaba da samun kudi.

Hakan ya sa Aminya ta rairayo wasu ’yan wasan da suka buga gasar Firimiyar Najeriya a kakar bara, amma yanzu sun fice zuwa kasashen ketare.

– Anayo Iwuala

Iwuala yana cikin matasan ’yan wasan kungiyar Enyimba ta Aba da ke Jihar Abia da ake ji da su.

Dan wasan ya koma kungiyar Espérance ta kasar Tunisia.

Iwuala ya buga wa Super Eagles wasa hudu a matakin ’yan wasan Super Eagles ’yan gida.

Yana cikin ’yan wasan da labarinsu ya yadu sosai bayan sun bar Firimiyar Najeriya din.

Anayo Iwuala Hoto: premiumtimes.com
– Bernard Ovoke

Ovoke dan wasan gaban Najeriya ne da ya koma kungiyar Sevan FC ta kasar Armeniya daga kungiyar Plateau United ta Najeriya.

A kakar bara, yana cikin ’yan wasan kungiyar ta Plateau United da suka nuna kwarewa matuka.

– Franklin Tebo Uchenna

Franklin Tebo Uchenna dan wasan Najeriya da ya je kungiyar Bollklubben Häcken, wadda aka fi sani da BK Häcken ko Häcken da ke birnin Gothenburg ta kasar Sweden a matsayin aro daga kungiyar Nasarawa United.

Franklin Tebo Uchenna Hoto daga owosport.com.ng
– Olisa Ndah

Ndah dan wasan bayan Najeriya ne da ya koma kungiyar Orlando Pirates ta kasar Afirka ta Kudu daga kungiyar Akwa United.

Dan wasan yana cikin ’yan wasan Najeriya a matakin ’yan wasan gida, inda ya buga wasa biyu, sannan ya buga wa Najeriya a matakin ’yan kasa da shekara 23.

Ya lashe gasar Firimiyar Najeriya tare da Akwa United a kakar bara kafin ya fice daga kasar.

Olisa Ndah Olisa Ndah hoto daga aoifootball.jpg
– Ibrahim Olawoyin

Ibrahim dan wasan kungiyar Enugu Rangers ta Najeriya ne a kakar bara da ya koma kungiyar Ankara Keçionrengucü ta kasar Turkiyya.

Dan wasan gaba da ya yi fice wajen santsi ga ’yan wasan baya, kuma yana cikin ’yan wasan Super Eagles na gida.

Ya buga wasan sa da zumunta na Najeriya da kasar Mexico da aka yi amfani da ’yan wasan gida kawai da aka buga a kasar Amurka.

Ibrahim Olawoyin hoto daga ACLSport.jpg
– Sunday Adetunji

Sunday Adetunji tsohon dan wasan gaban kungiyar Rivers United ne da ya koma kungiyar FC Shukupi ta Arewacin Macedonian.

Dan wasan ya buga wa Najeriya a matakin ’yan wasan kasa da shekara 23.

Sannan ya buga wa Super Eagles a matakin ’yan wasan gida, inda yake cikin ’yan wasan da suka fafata a wasan Najeriya da Mexico na sada zumunci a Amurka.

– ’Yan wasan mata 

Baya ga ’yan wasa maza, Aminiya ta kalato wasu ’yan wasa mata da suka bar Firimiyar Najeriya ta mata zuwa kasashen waje don ci gaba da taka leda.

Daga cikinsu akwai Glory Ogbonna ta koma kungiyar Umea ta Sweden daga kungiyar Edo Quens ta Jihar Edo da Margaret Etim ta kungiyar Rivers Angels da ta koma Cyprus da wasa da sauransu.

Gwamnatin Kano na shirin tara harajin 80bn a 2025

Kirsimeti: Zulum ya ɗauki nauyin jigilar fasinjoji 710 zuwa garuruwansu

Ɗan shekara 60 ya rasu a hatsarin kwalekwale a Sakkwato

Yadda gobara ta ƙone kasuwar babura a Zamfara