’Yan wasan Kano Pillars sun yi hatsarin mota

Ƙungiyar ta ce babu wanda ya rasa ransa a hatsarin motar.

’Yan wasan Kano Pillars sun yi hatsarin mota

Wasu daga cikin ’yan wasan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars, ’yan ƙasa shekara 19 sun jikkata a wani hatsarin mota da ya rutsa da su.

’Yan wasan na kan hanyarsu ta zuwa filin wasa na New Jos domin buga wasan mako na 5 na gasar matasa ’yan ƙasa da shekara 19 da Filato United.

Ofishin yaɗa labarai na ƙungiyar ya ce da dama daga cikin ’yan wasan da direbansu sun samu jikkata a hatsarin.

Kuma an garzaya da su asibiti don ba su agajin gaggawa.

“Abun farin ciki babu asarar rai a yanzu, kuma likitoci na kula da su sosai.

“Muna addu’a ga duk wanda lamarin ya shafa, kuma za mu sanar da ƙarin bayani game da lamarin.”