’Yan wasan kwallon kafa na wawure makudan kudi – FIFA
Wani bincike da Hukumar kwallon kafa ta Duniya (FIFA) ta gudanar ya gano cewa albashin da ake biyan ’yan wasan kwallon kafa ne ke daukar kaso mafi tsoka a lokacin da aka ci kasuwar sayen ’yan wasan kwallon kafa a shekara biyu da suka wuce.Binciken da Hukumar FIFA ta gudanar tun daga shekarar 2013, ta […]

Wani bincike da Hukumar kwallon kafa ta Duniya (FIFA) ta gudanar ya gano cewa albashin da ake biyan ’yan wasan kwallon kafa ne ke daukar kaso mafi tsoka a lokacin da aka ci kasuwar sayen ’yan wasan kwallon kafa a shekara biyu da suka wuce.
Binciken da Hukumar FIFA ta gudanar tun daga shekarar 2013, ta gano cewar ’yan wasan kwallon kafa da aka sayo daga wasu kungiyoyi sun karbi kashi 57 cikin 100 na cinikayyar ’yan kwallon da aka yi, yayin da kashi 41 cikin 100 ne gundarin kudin saye da sayar da ’yan kwallon da aka yi, kuma kudin masu kula da harkar kwallon ’yan wasa ya ci gaba da zama kashi biyu daga cikin 100.
Sai kuma kasshi hudu cikin 100 na kudin da kungiyoyin kwallon kafa na Turai suka kashe sun biya albashin ’yan wasa ne a lokacin da aka yi cinikayyar ’yan kwallon.
Binciken da aka yi a tsakanin shekara biyu ya nuna an biya ’yan wasan kwallo kafa albashin Dala biliyan 16 da rabi (kiminain Naira tiriliyan uku da biliyan 382 da rabi), inda Dala biliyan 12 (kimanin Naira tiriliyan biyu da miliyan 460) aka kashe kan saye da sayar da ’yan wasa, sai kuma Dala miliyan 700 (kimanin Naira biliyan 145 da rabi) aka bai wa wakilan ’yan kwallon a matsayin kamasho dinsu.