’Yan Yahoo sun harbe jami’in EFCC har lahira a bakin aikinsa

Ganin jami’an EFCC ke da wuya sa ’Yan Yahoo ɗin suka buɗe musu wuta, suka kashe wani mai muƙamin Mataimakin Sufurtanda, suka jikkata wani da raunin harbi a yayin da sauran jami’an suka sha da ƙyar.

’Yan Yahoo sun harbe jami’in EFCC har lahira a bakin aikinsa

Masu damfara ta intanet, waɗanda aka fi sani da ’Yan Yahoo, sun karbe wani jami’in Hukumar Yaƙi da Masu Karya Tattalin Arziƙin Ƙasa (EFCC), har lahira a bakin aikinsa.

’Yan Yahoo sun kashe shi tare da jikkata wani abokin aikinsa ne a yayin da shi da tawagar jam’an EFCC suka kai samame a wata matattarar ɓata-garin a Jihar Anambra.

Ganin jami’an ke da wuya sa ’Yan Yahoo ɗin suka buɗe wuta, suka kashe wani mai muƙamin Mataimakin Sufurtanda, suka jikkata wani da raunin harbi a yayin da sauran jami’an suka sha da ƙyar.

Aminiya ta gano cewa wanda aka jikkata yana kwance ranga-ranga ana jinyar sa a wani asibiti, da ba a bayyana ba.

An tura jami’an na EFCC aikin a Jihar Anambra ne daga babban Ofishin Hukumar da ke Enugu.

Da yake tabbatar da faruwar hakan, kakakin ’yan sanda na Jihar Enugu, Tochukwu Ikenga, ya ce, “muna gudanar da bincike, amma wanda ake zargin ya shiga hannu kuma mun ƙwace bindigar a hannunsa.”

Boko Haram sun ƙone makarantu a Borno

Har yanzu ’yan bindiga ba su saki matar Manjo Janar Rabe ba

An binne gawar Manjo Janar Rabe a Katsina

Wasu tsiraru ne ke rura matsalar tsaro a Najeriya — Christopher Musa