‘Yan Yahoo-Yahoo na sace dukiyar Turawa ne domin daukar fansa – Zakariya

Malam Muftah Zakariyya shi ne Sakataren Kungiyar Kare Hakkin Dan Adam ta Human Right Defenders and Adbocancy Centre na kasa, kuma Shugaban Kungiyar na Jihar Oyo. A tattaunawarsa da Aminiya, ya bayyana cewa binciken da suka gudanar ya nuna cewa, mafi yawan ‘yan Yahoo-Yahoo suna ikirarin cewa suna yi wa Turawa satar kudi na fitar […]

‘Yan Yahoo-Yahoo na sace dukiyar Turawa ne domin daukar fansa – Zakariya

Muftah Zakariyya

Malam Muftah Zakariyya shi ne Sakataren Kungiyar Kare Hakkin Dan Adam ta Human Right Defenders and Adbocancy Centre na kasa, kuma Shugaban Kungiyar na Jihar Oyo. A tattaunawarsa da Aminiya, ya bayyana cewa binciken da suka gudanar ya nuna cewa, mafi yawan ‘yan Yahoo-Yahoo suna ikirarin cewa suna yi wa Turawa satar kudi na fitar hankali ne domin daukar fansar irin bakar wahalar da suka gana wa bakaken fata a wancan lokaci. Ga hirar kamar haka:

 

Aminiya: Su wanene ‘yan yahoo-yahoo?

Zakariya: ‘Yan yahoo-yahoo wasu mutane ne matasa da suke ajiye kasumba da gemu a fuskarsu a matsayin wani nau’i na Kwamared masu fafutukar neman ‘yanci da hakkin bakaken fata da turawa suka bautar da su tare da azabtarwa da salwantar da jininsu. Shi ne yasa suke shiga cikin Yanar Gizo (Inernet) suna yi wa turawa satar kudade na fitar hankali domin daukar fansa kuma suna yin nasara a tsanake ba tare da sun damu ba.

Aminiya: Me ne ne matsayin kungiyarku a kan haka?

Zakariya: Matsayin Kungiyarmu shi ne ba zaka dauki matakin fansar zalunci da zalunci ba.

Aminiya: A wace kasa aka fi samun irin wadannan matasa ‘yan yahoo-yahoo?

Zakariya: Gaskiyar magana ita ce, Najeriya ce kan gaba a duk kasashen Afirka wajen samun wayayyun mutane masu hazaka da aiki da kwakwalwarsu ta fannoni daban-daban na rayuwar bil’adama. A Najeriya ne ake samun masu amfani da kwakwalwarsu wajen yin wasu ayyuka da na’ura mai kwakwalwa (Computer) ba za ta iya yinsu ba. Wannan ne yasa Najeriya ta zama a kan gaba wajen samun irin wadannan miyagun mutane ‘yan yahoo da suke bata sunan kasarmu a duniya.

Aminiya: Wace hanya kake ganin Najeriya za ta ci amfanin irin wadannan wayayyun mutane masu hazaka?

Zakariya: Da ace akwai wata hukumar kishin kasa da ta san mutuncin kanta da jama’arta a Najeriya, to da ita wannan hukuma ce za ta lalubo halastattun hanyoyi da za ta janyo irin wadannan mutane kusa da ita domin yin amfani da irin hazakarsu ta yadda kasa za ta amfana.

Aminiya: Wadanne irin hanyoyi ne ‘yan yahoo suke amfani da su wajen sace dukiyar turawa?

Zakariya: Hanyoyin suna da yawa kuma duka a cikin yanar gizo suke yin dabarun. Akwai daya daga cikin wadannan matasa wanda ya hadu da wata baturiya wacce ita kadai mahaifinta ya haifa ta yi gadon dimbin kudade da kadarori da wannan dan yahoo-yahoo ya yi dabarar tatuke dukiyar kaf, a sakamakon haka ta kashe kanta saboda bakin ciki. Na tambayi wannan yaro ko ka san cewa abun da ka aikata bai dace ba? Sai ya bani amsar cewa ai shi ya salwantar da ran bature daya ne kawai. Ko ka san yawan bakaken fata da turawa suka salwantar da rayukansu kafin mahaifinta ya samu wannan dukiya? Su a wurinsu suna ganin duk abun da suka yi ya dace, domin suna daukar fansa ne, wanda mu ba mu amince da irin wannan dankar fansa ba.

Aminiya: A bincikenku me kuka gano wadannan matasa suke yi da irin wannan dukiya domin amfanin jama’a?

Zakariya: Babu abun da suke yi da irin wannan dukiya sai bushasha da suke salwantar da su a banza ba tare da sun ci amfaninsu ba. Kamar yadda suke ikirarin cewa suna daukar fansa daga turawa, da ma ace suna yin amfani da dukiyar wajen bayar da tallafi ga gajiyayyu marasa galihu da daukar nauyin karatun kananan yara daga Firamare zuwa Jami’a ne, to ana iya cewa ba laifi ta wani fanni. Amma haka suke shiga cikin Kulob-Kulob suna alfasha da barnatar da kudi wajen yin gasar sayan kwalbar giya guda daya mai darajar kudi naira dubu 100 ana budewa ana zubarwa a kasa. Bincikenmu ya nuna cewa irin wadannan bangarori masu gasa a cikin Kulob suna kashe kudi fiye da naira miliyan daya a cikin dare daya kawai, domin kece raini a cikin Najeriya da wasu miliyoyin mutane suke neman naira daya ba su samu ba, amma ga wasu suna salwantar da kudi ba tunani. To ka ga kenan wayewarsu da hazakarsu da samun na su bai amfane su ba kuma bai amfani kasar su ba.

 

Aminiya: Wace shawara za ka ba Gwamnatin Najeriya a kan wannan al’amari?

Zakariya: A zamanin mulkin tsohon Shugaba Goodluck Jonathan an ware kudi fiye da dalar Amurka miliyan dubu 2 da sunan sayo makamai. Mu kaddara cewa an yi amfani da wannan kudi wajen yin muhimman abubuwan da za su amfanar da irin wadannan matasa ai ba laifi domin makami ba zai zama kariya ga al’umma ba. Abun da zai zama kariya shi ne mahukunta da jama’a su ladabtar da matasansu ta fannin yadda za su yi amfani da hazakarsu da za su kai ga gina kasa.