’Yan Yahoo-Yahoo sun yi bore kan kamen EFCC
An kashe mutum daya a tarzomar ’Yan Yahoo-Yahoo kan farautar su da jami’an EFCC ke yi a Jihar Delta.
An kashe mutum daya bayan gungun masu damfara ta intanet, wato ’Yan Yahoo-Yahoo sun yi bore kan farautar su da jami’an Hukumar Yaki da Masu Karya Tattalin Arziki (EFCC) ke yi a Jihar Delta.
Wani direba, Oke oghenkaro, ya ce ’Yan Yahoo-Yahoo din sun fusata ne bayan jami’an EFCC sun kai samame a maboyansu, wadanada suka rika fasawa suna shiga suna kama wasu daga cikinsu.
Zuwa lokacin kammala hada wannan rahoto, ba a kai ga gano ko wanda aka kashe din na daga cikin masu boren ba, kuma ’Yan Yahoo-Yahoo din sun tsere daga yankin na Otovwodo, don guje wa shiga hannun hukuma.
Hakazalika babu tabbacin ko jami’an EFCC sun je wurin tarzomar domin kama masu zanga-zangar.
Mazauna garin Ughelli dai sun yi tir da boren, sun kuma nuna damuwa bisa yyadda suka ce jami’an EFCC ke kai haramtattun samame, suna masu shawartar hukumar da ta rika gudanar da aikinta bisa ka’ida.
Ya ce, “Ba na shakkun fada cewa ’yan siyasa su ne manyan ’yan siyasa a kasar nan; Sun damfari bangaren ilimi da tattalin arziki da na tsaro da na samar da wutar lantarki sannan sun sace kadarorin gwamnai da albarkatun kasa da sauransu.
“Tun da EFCC na da hurumin bincikar dukiyar da aka samu a haramacciyar hana, to ya kamata ta bincika kuma magance kangin talaucin da aka jefa mutane a ciki.
“Yin fatara a Najeriya laifi ne ba don shugabanni ba su yi gaban kansu da dukiyar al’ummar kasa ba.
Wani direba, Oke oghenkaro, ya ce matasan sun fusata ne bayan jami’an EFCC sun kai samame a gidajensu suna fasawa suna shiga suna kama wasu daga cikinsu.
Waa mata a garin, Maro Franklin samamen na EFCC ne ya fusata masu boren suka yi wannan aika-aika.
Wakilinmu ya tuntubi kakakin ’yan sandan jihar, amma ya ce ba shi da labarin abin a a faru.