’Yan zanga-zanga sun wawushe kaya a shaguna a Kano
Sun banka wuta a ofishin Hukumar Sadarwa ta Kada (NCC) da ke Kano inda suka kwashe kwamfutoci da kujeru wasu kayan aiki.
Bata-gari sun far wa ofishin Hukumar Sadarwa ta Kada (NCC) da ke Kano inda suka kwashe kwamfutoci da kujeru wasu kayan aiki.
Masu tarzomar sun kuma cinna wuta a ofishin kafin daga bisani jami’an tsaro su kawo dauki a wurin.