’Yan ZAROTA na cin mutuncin ’yan PDP a Zamfara –’Yandoto
Babban Daraktan Yakin Neman Zaben Alhaji Mamuda Aliyu Shinkafi da ke takarar Gwamnan Jihar Zamfara a karkashin Jam’iyyar PDP, Alhaji Malami Aliyu ’Yandoto, ya zargi gwamnatin Abdul’aziz Yari Abubakar da amfani da matasan da ta dauka aiki wanda aka fi da ’yan ZAROTA wajen cin mutuncin jam’iyyun adawa a jihar. Alhaji Malami Aliyu ’Yandoto wanda […]
Babban Daraktan Yakin Neman Zaben Alhaji Mamuda Aliyu Shinkafi da ke takarar Gwamnan Jihar Zamfara a karkashin Jam’iyyar PDP, Alhaji Malami Aliyu ’Yandoto, ya zargi gwamnatin Abdul’aziz Yari Abubakar da amfani da matasan da ta dauka aiki wanda aka fi da ’yan ZAROTA wajen cin mutuncin jam’iyyun adawa a jihar.
Alhaji Malami Aliyu ’Yandoto wanda har wa yau dan takarar Mataimakin Gwamnan Jihar ne ya yi koken a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Gusau, inda ya yi zargin cewa matasan an dauke su ne da sunan za su taimaka a kan hanyoyi don rage cinkoson abubuwan hawa da kuma musu aiki amma an kwashe watanni babu wanda aka bai wa ko sisi.
Ya ce tun daga lokacin da tsohon Shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari ya je Jihar Zamfara, aka sanya ’yan ZAROTA suka rika karya allon takara da kuma fosta-fostan duk wani dan takara na Jam’iyyar PDP tun daga garin Gurbin Bore da ke iyaka da Jihar Katsina har zuwa Gusau.
dan takarar Mataimakin Gwamnan, ya yi kira ga gwamnatin Jihar Zamfara da Gwamnatin Tarayya su gaggauta daukar mataki kan abin da ke faruwa, kada gwamnati ta rike tana kallo, a jefa rayukan yaran cikin mawuyacin hali nan gaba.
Sai dai Gwamnan Jihar Alhaji Abdul’aziz Yari Abubakar ya dora alhakin wasu abubuwa da suke faruwa a jihar a kan jam’iyyar adawa ta PDP, ya ce wasu magoya bayan PDP ne idan suka shiga gari suke farfasa wa jama’a shaguna tare da lalata motocin mutane.
Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da yake yawon kaddamar da yakin neman zabensa a karamar Hukumar Maru, ya ce wannan abu da PDP ke yi tabarmar kunya ce suke nade ta da hauka, saboda tsohon Gwamna Shinkafi bai yi wa jama’a aikin kirki ba a baya. Ya bukaci magoya bayan Jam’iyyar APC su daure kada su tanka wa duk ya takale su, kuma kowane dan jihar ya karbi katin zabe don zaben jam’iyyar a zabe mai zuwa.