Yana fuskatar daurin shekara 37 kan zagin karen sarki
Wani dan kasar Thailand na fuskantar daurin shekara 37 saboda tuhumarsa da aibata karen Sarkin kasar, a wani sharhi da ya yi a shafin sadarwarsa na intanet, al’amarin da ya saba wa sauraran dokokin kasar da ta kare martabar Sarki. Mahukunta sun tsare mutumin wanda ma’aikacin wata masana’anta ne, mai suna Thanakorn Siripaiboo a gidansa […]
Wani dan kasar Thailand na fuskantar daurin shekara 37 saboda tuhumarsa da aibata karen Sarkin kasar, a wani sharhi da ya yi a shafin sadarwarsa na intanet, al’amarin da ya saba wa sauraran dokokin kasar da ta kare martabar Sarki.
Mahukunta sun tsare mutumin wanda ma’aikacin wata masana’anta ne, mai suna Thanakorn Siripaiboo a gidansa da ke wajen birnin Bangkok, a makon da ya wuce, inda suka tuhume shi da laifin rubuta munanan kalamai” ya baza a shafin intanet, game da Tongdaeng, wato karen Sarki Bhumibol Adulyadej, kamar yadda jaridar New York times ta ruwaito shekaranjiya Laraba.
Gwamnatin mulkin soja da ta yi juyin mulki a kasar a bara, har yanzu ba ta fayyace kowane irin laifi Thanakom ya yi ba.
Kare Tongdaeng, wanda sunansa ke nufin farin karfe, Sarkin na matukasr kaunarsa, kamar yadda mujallar Times ta ruwaito. A makon da ya wuce aka yi fim din Khun Tongdaeng, wanda ke nuni da rayuwarsa a cikin zayyana da aka tsakuro daga littafin tarihin Sarki Bhumibol, da aka rubuta a shekarar 2002 game da karensa.
Wannan tuhuma da ake yi wa Thanakum ita ce ta baya-bayan nan da aka ce an keta dokar kare martabar Sarki, wadda masana suka ce a ’yan kwanakin nan sai kara fadada take yi. Kuma a Disamban bara an kama wasu dalibai da suka yi ikirarin zagin Sarki, bayan sun gudanar da wani wasan kwaikwayo a kan rayuwar Sarkin.
’Yan jarida sun ruwaito a shafukan twiter game da rahoton mujallar Times, cewa, tuhumnar laifuffukan d aake yi Thanakun ba ta fito a jaridun kasar Thailand ba.