Yanayin kaka ya janyo faduwar farashin kayan gwari a Kudu

kungiyar  masu sayar da kayan gwari ta kasuwar Olubade da ke yankin Egbeda a Jihar Legas ta ce yanayin kaka da aka shiga a yankin Arewa ne ya janyo faduwar farashin kayan gwari a jihohin Kudu.Sakataren kungiyar Alhaji Abdullahi Usaini, ya shaida wa Aminiya  cewa faduwar farashin kayan gwarin ya faru ne  saboda  lokacin kaka […]

Yanayin kaka ya janyo faduwar farashin kayan gwari a Kudu

kungiyar  masu sayar da kayan gwari ta kasuwar Olubade da ke yankin Egbeda a Jihar Legas ta ce yanayin kaka da aka shiga a yankin Arewa ne ya janyo faduwar farashin kayan gwari a jihohin Kudu.
Sakataren kungiyar Alhaji Abdullahi Usaini, ya shaida wa Aminiya  cewa faduwar farashin kayan gwarin ya faru ne  saboda  lokacin kaka da aka shiga a yankin Arewa. Duk da cewa hakan abu ne da aka saba gani a kowace shekara idan yanayin kaka ya kunno kai, to amma na bana ya sha bamban da yadda aka saba gani.  “Misali a yanzu ana samun kwandon tumatir daga Naira dubu 2 zuwa dubu 3, shi kuwa tattasai ana sayar da shi Naira  dubu 3 zuwa dubu 4 ” Inji shi.
Ya kuma koka a kan rashin cika alkawarin da hukumomi suka yi na samar  musu da katafaren filin sauke kaya. “Har yanzu gwamnati ba ta cika alkawarin da ta yi na ba mu filin sauke kaya ba. Duk lokacin da muka kawo kaya mun rika rabe-rabe ke nan, saboda babu wani wadataccen filin saukewa. Muna rokon gwamnati ta cika alkawarin don saukaka hada-hadar kasuwanci a kasuwar” Inji shi.

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50