Yanayin Sanyi: Yadda masu shayi da masu koko da kosai ke ciniki

Ciniki da ribar da masu shayi da masu koko da kosai ke samu ta karu saboda yanayin sanyi.

Yanayin Sanyi: Yadda masu shayi da masu koko da kosai ke ciniki

Kakar masu shayi da masu koko da kosai a Kaduna ta yanke saka, inda ribar da suke samu take ta karuwa, saboda yadda mutane ke tururuwar da ake yi zuwa teburan masu shayi don cin taliya da shan shayi, a yayin da wasu ke yin dandazo a wurin masu koko da kosai mai zafi, domin dumama cikinsu saboda yanayin sanyi.

Masu koko da kosai da masu shayi sun bayyana cewa a halin yanzu da ake sanyi, cinikinsu da ribar da suke samu sun karu fiye da yadda suka saba.

Malam Nasir Kabir, wani mai shayi ne a Titin Bida da ke garin Kaduna, ya ce  masu zuwa neman shayi mai zafi a teburinsa, tun lokacin da sanyin ya fara shigowa a makon farko na wa Disamban 2021.

Ya ce “Yawancin kwastomomina direbobin bas din haya ne da ’yan acaba sai leburori da dalibai da ke fara zuwa rumfata tun daga misalin karfe 6.30 na safe domin su samu abin da za su duma jikinsu.

“A cikin mako daya da ya gabata cinikina ya ninku, kuma tsakani da Allah ina samun riba sosai a wannan sana’ar,” inji Malam Nasir.

Shi ma wani mai shayi a Layin Sakkwato, Isah Gambo, ya ce sai da ya dauki yara biyu su rika taimaka masa saboda yawan mutanen da ke zuwa rumfarsa domin shan shayi a halin yanzu.

“Ni ina dafa taliya, daya yaron na hada shayi, shi kuma dayan yana wanke-wanke.

“Kafin yanzu mutum 20 zuwa 30 ne kan zo su sha shayi a wurina a kullum, amma tun da aka fara sanyi, yawansu ya karu zuwa akalla mutun 50 a kullum,” inji Gambo.

Ya bayyana cewa ana sayar da kofin shayi a kan N50 zuwa N100, kwanon taliya kuma  N100 zuwa N250, gwargwadon bukatar mai saye.

Najib Saleh da ke sayar da shayi a Titin Marafa, ya ce akasarin kwastomominsa daliban Jami’ar Jihar Kaduna ne.

Najib ya ce, “Yawanci idan aka fara sanyi, kwastomomina wadanda akasarinsu dalibai ne kan zo tun da safe su karya kafin su shiga lacca.

“Wasu kuma sukan zo can da yamma idan sanyi ya karu. Da wannan sa’anar nake daukar dawainiyar iyalina.”

Wani mai haya da babur mai kafa uku, Musa Anche, ya ce yakan fito gida tun da misalin karfe shi na safiya ya zo teburin mai shayin ya sha kafin ya fara aiki.

“A matsayina na gwauro, ina yawan zuwa wurin masu shayi saboda yanayin sanyi,” a cewarsa.

Shi kuma wani mai haya da babur, Abdullahi Mujtapha, ya ce yanayin sana’arsa ya sa dole sanyi ya kama shi.

Shi ya sa ”Nek zuwa in sha shayi da taliya domin in ji dumi a jikina. Yanzu sanyi ake yi sosai; rigar sanyi da hula da kuma safa da nake sanyawa ba tare sanyi su sa in ji dumi yadda ya kamata,” inji Mujtapha.