Yanayin zafi ne ya haifar da tsadar kayan gwari a Gombe – Sani Waya
Wakilin ’yan Kasuwar Kayan Gwari na Gombe Alhaji Sani Waya, ya ce ruwan sama mai karfi da aka yi ne ya sa zafin kasa ya lalata fiye da kashi casa’in na kayan gwari tun a gonaki. Alhaji Sani Waya ya shaida wa Aminiya cewa, yanzu haka suna samun tattasai ne daga kasar Nijar da Jihar […]
Wakilin ’yan Kasuwar Kayan Gwari na Gombe Alhaji Sani Waya, ya ce ruwan sama mai karfi da aka yi ne ya sa zafin kasa ya lalata fiye da kashi casa’in na kayan gwari tun a gonaki.
Alhaji Sani Waya ya shaida wa Aminiya cewa, yanzu haka suna samun tattasai ne daga kasar Nijar da Jihar Katsina, yayin da tumatir kuma suke sayo shi daga kasar Kamaru, sai yanzu ne tattasai da ake nomawa a Karamar Hukumar Balanga a Jihar Gombe ya fara samuwa wanda yake nuna kayan zai iya yin sauki nan ba da dadewa ba.
“Da farko abin da ya fara kawo tsadar kayan gwari shi ne ruwan sama mai yawa da aka yi, zafin da kasar ta yi ne ya haifar da lalacewar amfanin gonar sannan da rashin noma shi sosai kamar yadda aka saba a baya saboda tsoron yanayin da ake ciki kada a noma da yawa ya lalace,” inji shi.
Ya kara da cewa da kayan ya yanke musu sai suka koma sayo shi daga garuruwan Jos da Katsina har ma daga kasar Nijar.
Wakilin ’Yan Kasuwar Kayan Gwarin ya ce duk da yankewar da kayan ya yi yana da sauki a kan bara, domin a bara suna sayar da solon buhun tattasai a kan naira dubu 25 amma yanzu bai wuce Naira dubu 17 ba.
Kwandon tumatir kuwa a bara Naira dubu 13 zuwa 15 har dubu 17 sun sayar, amma yanzu haka tsadarsa Naira dubu 8 har dubu 4 sun sayar a Sallar nan.
Ita kuwa albasa a cewarsa; ba ta kara kudi ba a kan yadda suke sayar da ita a barar, inda solonta yana nan a kan Naira dubu 6 zuwa dubu 6 da 500 zuwa dubu 7.
Alhaji Sani Waya, ya ce kada mutane su dauka saboda lokacin Sallah ne da aka fi bukatar kayan ya sa ya kara kudi, wadannan dalilan da ya bayyana ne a baya amma suna sa ran nan gaba kadan kayan zai samu kuma zai yi sauki.
Ya ce a shekarun baya daga nan Gombe har kasar Ghana da Kamaru suke shigar da kayan su amma yanzu saboda yadda ya yanke sai dai su ma su je Kamaru da Nijar su sayo, kuma a hakan da yake tattasai dan Balanga ya fara fitowa suna iya kaiwa jihohin Bauchi da Adamawa da Borno.
Ya yi kira ga sabuwar gwamnatin jihar ta Alhaji Muhammad Inuwa Yahaya ta kula da manoman kayan gwari kamar yadda gwamnatin baya ta yi nata kokarin.
Daga nan sai ya yi kira ga suma manoman da kada su yi kasa a gwiwa su kara himma wajen fadada noman don kauce wa tsadar kayan.