’Yancin bawa da fifikonsa:
Babi na Farko: ’Yanci da fifikonsa a Musulunci. Bisa fadar Allah Madaukaki cewa: “Ita ce fansar wuyan bawa. Ko ciyarwa, a cikin yini ma’abucin yunwa. Ga maraya ma’abucin zumunta” (k:90: 13-15):232. An karbo daga Ahmad dan Yunus ya ce: “Asim dan Muhammad ya ba mu labari ya ce, Wakid dan Muhammad ya ba ni labari […]
Babi na Farko: ’Yanci da fifikonsa a Musulunci. Bisa fadar Allah Madaukaki cewa: “Ita ce fansar wuyan bawa. Ko ciyarwa, a cikin yini ma’abucin yunwa. Ga maraya ma’abucin zumunta” (k:90: 13-15):
232. An karbo daga Ahmad dan Yunus ya ce: “Asim dan Muhammad ya ba mu labari ya ce, Wakid dan Muhammad ya ba ni labari ya ce, Sa’id dan Marjana abokin Aliyu dan Husain ya ce, “Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi) ya fada mini, cewa: Annabi (SAW) ya ce: “Duk mutumin da ya ’yanta wani mutum Musulmi, Allah zai kubutar da da gabbansa daga wuta shi bisa kowace gabarshi (bawa).” Sa’id dan Marjana, sai na tafi da shi (wannan labari) zuwa ga Aliyu dan Husain sai Aliyu dan Husain (Allah Ya yarda da shi) ya ’yanta bawansa da wannan fatawa wanda Abdullahi dan Ja’afar ya ba shi bisa dirhami dubu ko ya ce, dinari dubu amma ya ’yanta shi.”
233. An karbo daga Ubaidullahi dan Musa ya ce: “Daga Hisham dan Urwatu daga Babansa daga Abu Murawih daga Abu Zarri (Allah Ya yarda da shi), ya ce: “Na tambayi Annabi (SAW) wani aiki ya fi fifiko? Ya ce, “Imani da Allah da jihadi don daukaka kalmarSa.” Sai na ce, “Wace ’yantawa ne ta fi fifiko? Ya ce, “Wadda ta fi tsadar kudI kuma tafi soyuwa ga mai ita (bawa).” Na ce, “Idan ban iya aikata haka ba fa?” Ya ce, “Ka taimaki mai sana’a, ko ya ce, “ka kyautata koyar da mai sana’a don ya zama mutum mai sana’ar hannu.” Na ce, “Idan ban iya aikata (mallakar) haka ba fa?” Ya ce, “Ka tsare mutane daga sharrinka ita ma sadaka ce, gare ka a kanka.”
Babi na Biyu: Abin da aka so game da ’yanta bayi lokacin fakuwar rana ko wasu ayoyi na ban mamaki:
234. An karbo daga Musa dan Mas’ud ya ce: “Za’ida dan kuddama ya ba mu labari daga Hisham dan Urwatu daga Fadimatu ’yar Munzir daga Asma’u ’yar Abubakar (Allah Ya yarda da su) ta ce: “Annabi (SAW) ya umarta da ’yanta bayi a cikin yinin da aka yi fakuwar rana.” Aliyu ya karbo daga Darawardiyyu daga Hisham.
235. An karbo daga Muhammad dan Abubakar ya ce: “Assam ya ba mu labari daga Fadimatu ’yar Munzir daga Asma’u ’yar Abubakar (Allah Ya yarda da su) ta ce: “Mun kasance ana umartarmu da mu ’yanta bayi kyauta lokacin kusufin (fakuwar) rana.”
Babi na Uku: Idana aka ’yanta bawan da ke tsakanin mutum biyu, ko baiwar da take mallakar mutane:
236. An karbo daga Aliyu dan Abdullahi ya ce: “Sufiyan ya ba mu labari daga Amru daga Salim daga Babansa (Allah Ya yarda da shi) daga Annabi (SAW) ya ce: “Wanda ya ’yanta wani bawa wanda ke tsakanin mutum biyu to ya ’yanta shi gaba daya. Idan kuwa ya kasance mara shi (kudi) sai daga baya ya samu arzikin sai a yi masa kudi ya biya sa’an nan a ’yanta shi.”
237. An karbo daga Abdullahi dan Yusuf ya ce: “Malik ya ba mu labari daga Nafi’u daga Abdullahi dan Umar (Allah Ya yarda da su), cewa: “Lallai Manzon Allah (SAW) ya ce: “Wanda duk ya ’yanta bawan da suka yi tarayya da wani, kuma ya kasance na da abin da zai iya biyan sauran kudin bawan, to a yi kimar kudin bawan bisa daidaito (adalci) ya biya abokin tarayyarsa don biyan rabonsu ya ’yanta bawan idan ba haka ba, to ya ’yanta masa abin da yake iya ’yantawa.”
238. An karbo daga Ubaid dan Isma’il ya ce: “Daga Abu Usama daga Nafi’u daga dan Umar (Allah Ya yarda da su) ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya ce, “Wanda ya ’yanta rabonsa cikin abin mallaka (bawa), to yana kansa ’yanta shi gaba daya (dukkansa), idan yana da abin da zai iya biyan kudinsa. Idan ba ya da dukiyar ’yanta shi idan ya samu sai a yi masa kudin daidai ga mai ’yantawa, idan ba haka ba, ya ’yanta gare shi abin da yake iya ’yantawa.”
239. An karbo daga Musaddad ya ce: “Bishiru ya ba mu labari daga Ubaidullah ya takaita shi.